Daily Trust Aminiya - #EndSARS: Za a kori ‘Yan sanda 37, a gurfanar da 24
Subscribe

Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu

#EndSARS: Za a kori ‘Yan sanda 37, a gurfanar da 24

Hukumar kula da ‘Yan sanda ta Kasa (PSC) za ta kori jami’an tsohuwar rundunar SARS 37 tare da gurfanar da 24, bisa zargin aikata laifuka daban-daban da suka sabawa dokokin aiki.

Hakan dai na kunshe ne a rahoton da kwamitin binciken da shugaban kasa ya nada cikin shekarar 2018 domin kawo gyara da canje-canje a rundunar da kuma aikin ‘yan sanda a Najeriya.

Daga cikin abinda rahoton ya kunsa dai kwamitin ya yi bincike kan koke-koke da zarge-zargen da mutane suka gabatar na take hakkin bil’Adama da karya dokokin aiki, tare kuma da bijiro da hanyoyin da za a bi domin kawo gyara a rundunar.

Da ya ke gabatar da rahoton kwamitin ga shugaban PSC, Musiliu Smith, a Abuja, ranar juma’a, Babban Sakataren Hukumar Kare Hakkin Bil’Adama ta kasa (NHRC), Tony Ojukwu, ya roki PSC ta gaggauta aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya bayar.

A Takardar da Kakakin Hukumar Kula da ‘Yan sanda (PSC), Ikechukwu Ani, ya fitar, ya ce Ojukwu ya bada tabbacin cewar shugaban PSC na da kwarewar da zai aiwatar da rahoton ta hanyoyin da suka dace.

“Mun zo mu ga yadda PSC za ta tsaya, ta taka rawa domin ganin an samu sauye-sauye cikin aikin ‘Yan sanda Najeriya inji Ojukwu,” inji takardar.

Ya kara da cewa a yanzu ra’ayin al’ummar kasa ya karkata ne wajen ganin an kawo canje-canje a aikin yan sanda yan mai cewa idanun al’umma na kan hukumar.

Ikechukwu ya kuma ce hukumar ta karbi korafe-korafe guda 113 a fadin kasar nan da suka shafi take hakkin bil’Adama da kuma shawarari 22 da za su taimaka wajen kawo gyara a rundunar ta SARS da ma aikin ‘yan sanda baki daya.

“Bayan an kammala sauraren korafe-korafen mutane, kwamitin ya bayar da shawarar a sallami ‘yan sanda 37, a kuma hukunta 24,” inji sanarwar.

Taken takarda da kakakin hukumar ya fitar shi ne: ‘PSC tare da hadin gwiwar NHRC, ta yi alkawarin daukar matakin gaggawa kan rahoton da kwamitin shugaban Kasa ya fitar a kan SARS’.

More Stories