✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Eriksen zai koma United da taka leda

Za a bai wa dan wasan yarjejeniyar kaka uku idan an kammala tabbatar da koshin lafiyarsa.

Dan kwallon tawagar Denmark, Christian Eriksen ya amince zai saka hannu kan yarjejeniyar komawa Manchester United da taka leda.

Kwantiragin dan wasan mai shekara 30, ya kare a Brentford a kakar tamaula da aka kammala a watan jiya.

Bayanai dai sun nuna cewa dan kwallon yana da damar ci gaba da taka leda a kungiyar da Thomas Frank ke jan ragama, amma ya zabi ya koma United.

Fabrizio Romano, kwarren dan jarida kan sha’ananin kwallon kafa, ya ce za a bai wa dan wasan yarjejeniyar kaka uku idan an kammala tabbatar da koshin lafiyarsa a Old Trafford.

Eriksen ka iya zama na biyu da sabon koci, Erik ten Hag zai dauka a bana, bayan da kungiyar ke auna koshin lafiyar dan wasan Feyenoord, Tyrell Malacia a shirin komawa United da yake yi.

Eriksen ya koma buga Firimiyar Ingila, bayan da Brentford ta dauke shi a watan Janairu, bayan barin Inter Milan mai buga Serie A.

Ya bar buga gasar Serie A, bayan da aka dasa masa na’urar da ke taimaka masa yin nunfashi, hakan doka ne a babbar gasar Italiya, ba zai buga wasanni ba.

Ana iya tuna cewa, Eriksen ya yanke jiki ya fadi a lokacin da yake yi wa tawagar Denmark wasa a Euro 2020, gasar da Italiya ta lashe.

Tsohuwar kungiyar Eriksen, Tottenham wadda ya yi mata tamaula tsakanin 2013 zuwa 2020 ta so daukar dan wasan, amma ba ta mayar da hankali ba.