✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EU ta haramta amfani da motoci masu amfani da fetur da gas

Matakin zai yi illa ga kasashen da suka dogara da mai don samun kudin shiga.

Majalisar Tarayyar Turai, ta amince da haramta sayar da motocin da ke fitar da gurbataccen hayaki masu amfani da man fetur da kuma diesel nan da shekara ta 2035.

Wannan mataki na Majalisar Tarayyar Turai dai, ya nuna cewa, abin da ya rage shi ne sanya hannu kan wannan kudiri ya kuma zama doka.

Koda yake wannan mataki na fuskantar turjiya daga bangaren masu ra’ayin ’yan mazan jiya da ke da rinjaye a majalisar.

Ya zuwa yanzu dai kudirin ya samu amincewa daga mambobi 340 yayin da 279 suka nuna kin amincewa kana 21 suka yi rowar kuri’unsu.

Kasashen duniya da suka ci gaba ta fannin kimiyya da fasasha na ci gaba da bayyana shirinsu na kera motoci masu amfani da wutar lantarki, abin da zai kawo karshen motocin da ke amfani da man fetur ko kuma dizil.

Tun a shekarar 2017 Birtaniya ta sanar da shirinta na kawo karshen siyar da motocin da ke amfani da man fetur da diesel nan da shekarar 2040, bayan Faransa ta sanar da makamancin matakin a cikin watan Yulin 2017 da zimmar rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli.

A shekarar 2016 ce dai, China ta gabatar da nata shirin da ya bukaci siyar da kashi 12 cikin 100 na motoci da ke amfani da batir zuwa shekarar 2020.

Ita ma India tun a wancan lokaci ta ce, nan da shekarar 2030 ne ta ke fatan fara amfani da motoci masu aiki da wutar lantarki.

Kazalika, kasar Norway na da irin wannan burin na kawo karshen siyar da motoci masu aiki da man fetir nan da shekarar 2025, kamar yadda su ma Sweden da Denmark da Finland duk suka sanar da irin wannan shiri.

A dalilin yunkurin wadannan kasashe ne, wani Farfesa kan ilimin kimiya da fasasha a Jami’ar York, Alastir Lewis, ya yi hasashen cewa, nan da shekarar 2040, injinan kananan motoci masu fitar da hayaki za su bace da kansu ba tare da gwamnati ta tabuka wani abu ba.

Sai dai wasu masana na ganin cewa, matakin zai yi illa ga kasashen da suka dogara da mai don samun kudin shiga.