✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EU ta umarci jami’anta su fice daga Ukraine

Jakadan EU a Ukraine, Matti Maasikas, ya umarci ma'aikata su su koma aiki daga wajen kasar

Tarayyar Turai (EU) ta umarci jami’anta da su fice daga kasar Ukraine a bayan rikicin Rasha da Ukraine ya kara kamari a baya-bayan nan.

Umarnin na zuwa ne bayan Amurka da Birtaniya sun umarci ’yan kasashensu da su fice daga Ukraine, a yayin da fadar White House ta Amurka ke zargin nan gaba kadan Rasha za ta kutsa cikin Ukraine.

A ranar Juma’a Jakadan EU a Ukraine, Matti Maasikas, ya tura sako cewa, “Duk ma’aikata, in banda masu matukar muhimmanci… su bar Ukraine da sauri su koma aiki daga wajen kasar.”

Duk da haka EU ba ta bayar da umarnin kwashe ma’aikatan jakadancinta daga Ukraine, wadda ke wa juna kallon hadarin kaji da Rasha da ake fargabar tana neman mamaye ta.

Wani jami’in EU, Peter Stano, ya ce, “Muna kara lura da abin da ke faruwa gwargwadon aikinmu na kare jami’anmu da hadin gwiwar kasashen EU.

“A halin yanzu an ba wa kananan ma’aikata damar yin aiki daga wajen kasar, amma ba za su fice gaba daya ba tukuna.”

A shekarar 1993 EU ta fara tura jakadunta zuwa Kyiv, babban birnin kasar Ukraine, domin kulla dangantaka tsakanin kungiyar da kasar.