✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

EURO 2020: Babu dan wasan Real Madrid a tawagar Spain

Luis Enrique ya cire Sergio Ramos daga cikin ’yan wasan Spain a EURO 2020.

A ranar Litinin kocin ’yan kwallon kafar kasar Spain, Luis Enrique, ya fitar da jerin ’yan wasan da za su wakilci kasar a gasar Euro 2020, amma abun mamaki babu dan wasan Real Madrid ko daya a ciki.

Kyaftin tin Spain, Sergio Ramos na daga cikin ’yan wasan Real Madrid da kocin ya ajiye sakamakon rauni da ya sha fama da shi a wannan shekara.

Tuni Sergio Ramos, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, “Tabbas na yi bakin cikin rashin zuwana gasar saboda ba zan taimaka wa kasata ba, amma ina fatan zan koma gida na huta domin warwarewa yadda ya kamata, sannan na dawo fage daga badi don wakiltar kasata ta Spain.

“Ina yi wa abokaina da kasata fatan nasara a gasar Euro kuma zan ci gaba da goyon bayan kasata daga gida”, cewar Ramos.

Tuni dai masu sharhi suka shiga tofa albarkacin bakinsu kan rashin kiran dan wasa ko daya da Luis Enrique ya yi daga Real Madrid, don wakiltar Spain a gasar EURO 2020.

Ga jerin ’yan wasa 24 da kocin Spain din ya kira don wakiltar kasar:

Masu tsaron raga: Unai Simon da David de Gea da kuma Robert Sanchez.

’Yan wasan baya: Jose Gaya da Jordi Alba da Pau Torres da Aymeric Laporte da Eric Garcia da Diego Llorente da Cesar Azpilicueta da kuma Marcos Llorente.

’Yan wasan tsakiya: Sergio Busquets da Rodri da Pedri da Thiago da Koke da kuma Fabian Ruiz.

’Yan wasan gaba: Dani Olmo da Mikel Oyarzabal da Alvaro Morata da Gerard Moreno da  Ferran Torres da Adama Traore da kuma Pablo Sarabia.