✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

EUROPA: Barcelona ta yi waje da Napoli

Barcelona ta doke Napoli har gida da ci 4 da 2.

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta bi Napoli har gida ta lallasa ta da ci 4 da 2 a gaban magoya bayanta.

Da sakamakon wannan wasa da aka kara a daren ranar Alhamis dai, tuni Barcelona ta wuce zagaye na gaba a Gasar Europa.

Kungiyoyin biyu sun tashi 1 da 1 ne a wasan farko da suka gwabza a filin wasa na Barcelona, wato Nou Camp, da ke birnin Catalonia a kasar Spain.

Jordi Alba, Frenkie de Jong, Gerard Pique da kuma Pierre-Emerick Aubameyang ne suka ci wa Barcelona.

Insigne da Politano su ne suka ci wa Napoli kwallonta biyu.