✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Everton ta kunyata Arsenal a Goodison Park

Arsenal ta yi rashin nasara ta biyu ke nan a kakar Firimiyar Ingila ta bana.

Arsenal ta kwashi kashinta a hannun yayin da ta je bakunta a wasan Firimiyar Ingila har gidan Everton a wannan Asabar din.

Wannan dai ita ce rashin nasara ta biyu ke nan da Arsenal ta yi a kakar Firimiyar Ingila ta bana.

Everton dai ta jefa wa Arsenal kwallo daya tilo a raga ta hannun James Tarkowski da ya bai wa kungiyar nasara a filin wasa na Goodison Park.

Masu masaukin bakin sun shiga fafatawar ce bayan rashin nasara takwas cikin wasanni 9 da suka buga a bayan nan.

Sai dai kungiyar ta samu karin karsashi a wasan a karkashin jagorancin sabon kociyan da ta dauka, Sean Dyche.

Everton dai ta dagula wa Arsenal lissafi yayin da daure tsakiyarta domin hana ruwa gudu, lamarin da ya sanya ’yan wasanta irinsu Thomas Partey, Granit Xhaka da Martin Odegaard suka gaza tabuka komai sabanin yadda suka saba a wasannin baya.

Kungiyar wadda Mikel Arteta ke jagoranci ta saba lugwigwita abokan karawarta cikin salo, amma dai lamarin ya sha bamban inda ’yan wasan gabanta irinsu Eddie Nketiah da Bukayo Sako suka rika barar da damarmaki.

Kamar yadda alkaluma suka tabbatar, wannan ita ce rashin nasara ta uku da Arsenal ta yi a jere a Goodison Park.

Haka kuma, kungiyar ta Arewacin Landan ta barar da damar ninka tazarar da da ke tsakaninta da Manchester City da ke zaman ta biyu a teburin Firimiyar Ingila.

Da zarar City ta yi nasara a wasan da za ta fafata da Tottenham a ranar Lahadi, zai rage maki biyu kacal tsakanin da Arsenal mai jan ragama a teburin Firimiyar na bana.

Sai dai duk da haka, Arsenal wadda ake yi wa lakaba da Gunners tana da kwantan wasa daya, wanda za ta yi fatan lissafi ya yi mata yadda take so.