✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Facebook ya kaddamar da manhajar gano yaran da suka bace a Najeriya

Manhajar za ta taimaka wajen gano yara ta Facebook da Instagram

Kamfanin Meta, mamallakin Facebook da Instagram ya kaddamar da manhajar da za ta taimaka wajen gano yaran da suka bace a Najeriya.

Manhajar, mai suna ‘AMBER Alerts’, an kirkiro ta ne tare da hadin gwiwar Hukumar Yaki da Safarar Bil-Adama ta Najeriya (NAPTIP).

Da zarar NAPTIP ta fara amfani da wannan manhajar dai, wata kararrawar sanarwa za ta rika bayyana a shafukan masu amfani da Facebook da Instagram a Najeriya don a gano yaran.

Daraktan Kiyaye Hadura na kamfanin Meta, Emily Vacher, yayin kaddamar da manhajar ranar Alhamis a Abuja ya ce, “Yanzu haka wannan manhajar na aiki a kasashe 28 a fadin duniya, kuma muna alfaharin hada gwiwa da NAPTIP wajen ganin AMBER ta fara aiki a Najeriya, wacce za ta kasance kasa ta biyu a Afirka da ta fara amfani da ita.”

Ita kuwa Shugabar hukumar ta NAPTIP, Fatima Waziri-Azi, ta ce manhajar ta zo a lokacin da aka fi bukatar ta, saboda karuwar matsalar batan yara a Najeriya.

“A bara kawai, NAPTIP ta ceto yara 13 da aka yi garkuwa da su, inda ta sada 12 daga cikinsu da iyayensu, dayan kuma har yanzu yana hannun masu garkuwar.

“Amma yanzu da wannan manhajar, nan da nan mutane za su taimaka wajen cigiya da gano yaran da suka bace. Wannan kawancen da kamfanin Meta zai yi tasiri matuka a yunkurinmu na ceto yara,” inji ta.