✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Facebook ya shiga tsaka mai wuya kan yada labaran karya

An fallasa yadda ake yada labaran karya da kulla makirce-makircen ta Facebook.

Kamfanin Facebook ya kara shiga rikici bayan bullar sabbin bayanai da ke nuna yadda yake bari da gangan ana amfani da kafafensa wajen kulla makirci da kuma yada labaran karya.

Kamfanin na neman kwatar kansa ne bayanan an samu karin masu kwarmato da suka fitar da bayanai kan yadda kamfanin ke kin daukar mataki a kan masu yada labaran karya da kulla makirci ta kafarsa, duk da cewa ma’aikatansa sun ja hankalinsa tare da nuna dumarsu a game da matsalar.

Masu kwarmaton na zargin kamfanin ya bari da gangan ana yada kalaman batanci da haramtattun abubuwa, duk da cewa ma’aikatansa sun sha nuna damuwar kan yada karairayi, musamman a kan zabuka.

Zarge-zargen na masu fallasan da suka zanta da kafar yada labarai ta Washington Post, na cikin wani kundin korafe-korafen da aka aike wa Hukumar Hadahadar Hannun Jari ta kasar Amurka (SEC).

Wani tsohon ma’aikacin Facebook ya yi zargin cewa jami’an gudanarwar kamfanin na kin daukar matakan hana abubuwa da ba su dace ba ne saboda gudun fusata tsohon shugaban Amurka, Donald Trump da makusantansa, gami da gudun kawo tsaiko ga kudaden shigan kamfanin.

Tsoffin ma’aikatan kamfanin sun ambato wani lokaci da jami’in sadarwar kamfanin, Tucker Bounds, ya yi watsi da zargin rawar da kamfanin ya taka wajen magudin zaben 2016 a kasar Amurka.

“Wannan zai fusata wasu ’yan majalisa. Cikin ’yan makonnin cibi zame mana kari. Mu da ke karkashin kasa muna samun kudi, ina ruwanmu?” Inji Bonds kamar yadda takardar shaidar Washington Post ta ruwaito shi yana cewa.

Zargin na sabbin masu kwarmakon ya zo daidai da na tsohuwar manajar tallace-tallacen kamfanin Frances Haugen, cewa kamfanin ya fifita samun riba a kan maslahar al’umma.

Shaidar Haugen ta baya-bayan nan a gaban Majalisar Wakilan Amurka da irinta da za ta bayar a majalisar Birtaniya ya sa kimar Facebook na tangal-tangal, har kamfanin ya fara neman hanyoyin sake gyara sunansa.

A photo illustration of the Facebook logo.
Tambarin Facebook.
Shaidar da Haugen ta yi na zuwa ne a daidai ranar da kafafen yada labarai da dama, irin su New York Times, Washington Post da NBC, suka fitar da rahotonsu bisa dogaro da takardun shaidar da ta bayar.

Takardun sun ba da zurfafan bayanai game da labaran karya da aka yada da kuma makirce-makircen da aka kulla ta Facebook a lokacin zaben shugaban kasar Amurka na 2020.

Sun kuma nuna yadda ma’aikatan kamfanin suka sha nuna damuwa a lokacin zaben da bayansa, a yayin da Trump yake neman murde nasarar Joe Biden a zaben.

Rahoton New York Times, ya ce mako guda bayan zaben, wani masanin kididdigar kamfani ya shaida wa abokan aikinsa cewa kashi 10 cikin 100 na abubuwan siyasa da aka wallafa a Facebook na shaci fadi ne cewa an yi magudin zabe.

Da jin haka, ma’akatan Facebook suka ja hankalin kamfanin ya dauki mataki, amma ya ki, kamar yadda New York Times ta bayyana.

Masu bincike a Facebook sun kuma gano yadda kafar ta rika neman tura masu amfanin da ita zuwa shafukan masu tsattsauran ra’ayin, wanda hakan ya sa ma’aikata jan hankalin manajoji da shugabannin kamfanin, amma suka yi biris da su, inji rahoton NBC News.

A wani binciken cikin gida, wani binciken Facebook, ya kirkiri shafin karya da sunan “Carol Smith”, wata mace mai tsattsauran ra’ayi da ke son Fox News da Donald Trump.

Binciken ha gano cewa a cikin kwana biyu algorithm din Facebook na shawartar “Carol” ta shigar zauren QAnon, wanda ke kulla makirce-makirce marasa tushe a intanet.

Hakan ta faru ne a yayin da Facebook ke fuskantar karin matsin lamba daga ’yan majalisar wakilan Amurka da ke kokarin yin dokoki, gami da wani kara da antoni janar na kasar ya shigar, da kuma Hukumar Kula sa Kasuwanci wanda shugabar hukumar, Lina Khan ta shigar.

Frances Haugen, a former Facebook employee turned whistleblower, testifies before US lawmakers.
Frances Haugen, tsohuwar ma’aikaciyar Facebook da ta zama mai kwarmato, a lokacin da take ba da shaida a gaban Majalsiar Dokokin Amurka. (Hoto: Lenin Nolly/NurPhoto/REX/Shutterstock).

Masu sa ido a kan Facebook sun ce fallasar ta nuna matukar bukatar yi wa kafar Facebook linzami.