✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fada na kara kazancewa tsakanin dakarun Afghanistan da Taliban

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Aurka da NATO ke shirin janyewa.

Akalla yankuna uku da ke Kudanci da Yammacin Afghanistan ne yanzu haka ke fuskantar matsananciyar matsalar tsaro a daidai lokacin da fada ya dada kazancewa tsakanin dakarun Afghanistan da mayakan kungiyar Taliban.

Rikicin ya dada kazancewa ne a kasar da ke Kudancin nahiyar Asiya wacce yaki ya daidaita, a daidai lokacin da dakarun Amurka da na kungiyar kawance ta NATO ke shirin janyewa daga kasar a karshen watan Agusta bayan shafe shekara 20 suna fafata yaki.

Taliban dai na yunkurin kwace iko ne da manyan biranen lardunan kasar bayan da ta sami nasarar kwace kauyuka da dama a cikin ’yan watannin nan.

Shugaban Kasar ta Afghanistan, Ashraf Ghani dai na zargin janye dakarun Amurka daga kasar da rana tsaka da cewa shine ummul-aba’isun kara dagulewar al’amura.

To sai dai a nata bangaren, Taliban a cikin wata sanarwa da ta fitar a martaninta ga shugaban ta bayyana kalaman nasa a matsayin shiririta da kuma yunkurin yin rufa-rufa ga kura-kuren da ya tafka.

Ana tafka fada a Kandahar

Gidan talabijin na Aljazeera ya rawaito cewa an shafe daren ranar Lahadi ana tafka kazamin fada tsakanin dakarun bangarorin biyu a yankin Kandahar, kuma an fuskanci wani sabon rikicin a garin Boldak da ke kan iyakar kasar da Pakistan.

“Babban abin fargabar yanzu shine ana ci gaba da tafka fada tsakanin Taliban da dakarun gwamnati a cikin birnin Kandahar. Sojojin Afghanistan sun rika kai hari da jirage ta sama, inda suka ce sun kashe ankalla ’yan Taliban 35 cikin dare, amma har yanzu Taliban din bata mayar da martani ba,” inji wakilin Aljazeera a Kabul.

Abubuwa sun tabarbare a Helmand – Sojoji

Kakakin rundunar sojin kasar, Janar Ajmal Omar Shinwari a ranar Lahadi ya ce lamura sun tabarbare matuka musamman a garin Lashkar Gah na yankin Helmand, a inda suka kaddamar da hare-hare da nufin fatattakar mayakan Taliban.

Hukumomin lardin na Helmand sun ce Taliban ta kara yawan dakarunta a Lashkar Gah ranar Lahadi inda suka ce yanzu mayakan kungiyar ne ke iko da birane bakwai a lardin.

Birinin Kandahar na Kudancin kasar dai wanda nan ne tushen Taliban da Helmand da kuma Herat sun kasance cibiyar rikice-rikice a kasar.