✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fada ya barke tsakanin mayakan Ansaru da ’yan bindiga a Birnin-Gwari

Ba za a iya tantance yawan ’yan bindiga da Ansaru da aka kashe a fadan ba

Musayar wata ta barke tsakanin ’yan kungiyar Ansaru da ’yan bindigar da suka kai musu hari a yankin Birnin-Gwari na Jihar Kaduna.

Shugaban Kungiyar Hadin Kan Masarautar Birnin-Gwari, Ishaq Usman Kafai, ya ce kawo yanzu ba a kai ga tantance yawan ’yan bindiga da ’yan Ansaru da aka kashe a fadan ba.

Ya shaida wa Aminiya cewa “An yi barna a lokacin fadan — an kona wani shago da motoci biyu da wani asibiti mai zaman kansa;

“’Yan bindiga sun kuma kashe wasu leburori biyu a lokacin da suke tserewa zuwa cikin daji,” amma ya bayyana cewa asibitin ya kone ne a sakamakon wutar da ta tashi daga wata mota da aka cinna wa wuta.

Shaidu sun ce ’yan Ansaru na tsaka da yi wa jama’a ‘wa’azi’ a kauyen Damari ne ’yan bindiga suka je suka bude musu wuta, a garin haka suka kashe wasu mutum biyu.

Kafai ya ce an shafe kimanin awa guda ana ba-ta-kashi a tsakanin bangarorin biyu, amma daga baya ’yan Ansaru suka fatattaki ’yan bindigar daga kauyen.

Aminiya ta gano cewa fadan ya sa daruwan mazauna yankin, msuamman mata da kananan yara sun yi kaura domin samun tsira.

Kafai ya ce ’yan kauyen sun yaba da yadda ’yan Ansaru suka kare su daga harin ’yan bindiga.

Ya bayyana cewa bayan kurar ta lafa, mayakan na Ansaru sun ci gaba da wa’azinsu tare da kiran mazauna kauyen da su mallaki makamai domin kare kansu daga makiya da kuma gwamnati domin kafa ‘gwamnatin Musulunci’.

Mun nemi jin ta bakin kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, amma ya yi mana alkawarin bincikawa ya ji ainihin abin da ya faru kafin daga baya ya neme mu.

Majiyoyi sun ce mayakan Ansaru sun shiga kauyen na Damari da ke yankin Kazage a Gabashin Karamar Hukumar Birnin Gwari ne da nufin korar ’yan bindiga.

A baya mun kawo rahoton yadda kungiyar Ansaru ta yi kaka-gida a kauyukan Gabashin Karamar Hukumar Birnin-Gwari ta Jihar Kaduna, da sunan ba wa mazauna ‘kariya’ daga ’yan bindiga.