✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fadar Buckingham ta fara zaman makokin Sarauniya Elizabeth II

Sarki Charles III ne ya ayyana zaman makokin ga iyalan gidan sarautar, har sai bayan kwana bakwai da kai mahaifiyar tasa makwancinta.

Fadar Buckingham ta kasar Birtaniya ta fara zaman makoki a ranar Juma’a bayan rasuwar Sarauniya Elizabeth II, wadda ta shekara 73 a kan karagar mulki.

Sarki Charles III ne ya ayyana zaman makokin ga iyalan gidan sarautar, har sai bayan kwana bakwai da kai mahaifiyar tasa makwancinta.

Sanarwar da Fadar Buckingham ta fitar ta ce, “Sakamakon Rasuwar Sarauniya Mai Daraja, Mai Alfarma Sarki yana fata za a fara zaman makoki daga yanzu zuwa kwana bakwai bayan jana’izar.

“Nan gaba za a sanar da bayanan gudanar da jana’izar” mahaifiyar tasa.

Baya ga iyalan gidan sarautar, ma’aikata da jami’an tsaron fadar za su bi sahu a lokacin makokin.

A tsawon lokacin, za a saukar da tuta kasa-kasa a gidajen sarautar har zuwa washegarin jana’izar.

Za a yin harbin bindiga 96, daidai yawan shekarun marigayiywar a duniya, a ranar Juma’a da misalin karfe 1 na rana agogoin GMT a dandalin Hyde Park da ginin Tower of London.

Za kuma a rufe gidajen sarautar har zuwa bayan jana’izar.

Jami’an fada sun shawarci masu son ajiye furanni a Fadar Buckingham da su yi hakan a wani wuri da aka ware a dandalin Green Park da kuma Hyde Park.

Za kuma a bude littafin karbar ta’aziyya a shafin masarutar ta intanet kuma, gwamnatin kasar Birtaniya za ta bayar da sanarwar gudanar da jana’izar.