✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fadar Shugaban Kasa ta fadi sabuwar ranar da Buhari zai tafi Landan ganin likita

Fadar ta ce ranar Lahadi Buharin zai wuce Landan.

Fadar Shugaban Kasa ta ce har yanzu tafiyar da aka tsara Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai yi zuwa birnin Landan don ganawa da likitocinsa tana nan daram.

Mutane da dama dai sun bayyana mamakinsu kan yadda Shugaban ya dawo Abuja daga kasar Kenya, a maimakon birnin Landan kamar yadda aka sanar da farko.

Buhari dai ya halarci wani taro ne a birnin Nairobi na kasar Kenya kan cika shekara 50 da kafa Shirin Muhalli na Majalisar Dinkin Duniya (UNEP), inda daga can ne aka tsara zai wuce Landan din don ganin likitocinsa.

A farkon makon nan ne dai Hadimin Shugaban Kasa kan Yada Labarai, Femi Adesina ya sanar da cewa Buharin zai wuce Landan don ganawa da likitocinsa daga Kenya.

“Daga kasar Kenya, Buhari zai wuce Landan don ganawa da likitocinsa na tsawon mako biyu,” inji Adesina a cikin sanarwar.

Sai dai a ranar Juma’a, Bashir Ahmad ya tabbatar da cewa Shugaban ya dawo Abuja.

“Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dawo Abuja bayan ya halarci taron bikin cikar Shirin Muhalli na Majalisar Dinkin Duniya (UNEP) shekara 50a Kenya.

Sai dai mutane da dama sun fara nuna kokwantonsu tare da neman karin bayani kan musabbabin sauya shawarar.

Aminiya ta gano cewa Buhari ya sauka ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe 1:00 na rana.

Sai dai da wakilinmu ya tuntubi mai magana da yawun Shugaban, Malam Garba Shehu, ya shaida masa cewa Buhari ya dawo ne bayan an kammala taron na birnin Nairobi.

Da aka tambaye shi ko Shugaban ya fasa tafiyar ne gaba daya, sai ya ce, “Ko daya, bai dage tafiyar ba. Har yanzu tana nan kamar yadda aka tsara. Ya kammala abin da ya kai shi Kenya, Landan kuma sai ranar Lahadi zai tafi.