✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fadar Shugaban Kasa ta fara nazarin sake rufe iyakokin Najeriya

A bisa gwaji yanzu mun sake budewa da fatan cewa yarjejeniyar da muka kulla da su za ta yi tasiri.

Gwamnatin Najeriya a ranar Talata ta sanar cewa ta fara duba yiwuwar sake rufe iyakokin kasar da ta bude kwanan nan a sakamakon yadda ’yan ta’adda da kananan makamai ke kwararo wa cikin kasar.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ne ya sanar da hakan yayin hirar da ya yi a wani shiri na Sunrise Daily wanda gidan talbijin na Channels ya saba haska wa.

Gwamnatin ta ce tana ci gaba da nazari a kan al’amuran da suke faruwa cikin al’ummomin da ke kan iyaka da kasar Najeriya, lamarin da ta ce da yiwuwar za ta rufe iyakokin na ta muddin aka ci gaba da samun tangarda.

Mallam Garba ya ce Gwamnatin Najeriya ta lura cewa kasashen da ke makwabtaka da ita ba su ba da hadin kai ba wajen dakile kwararowar ’yan ta’adda da kuma kananan makamai, wanda a cewarta hakan na kara rura wutar ta’addanci a kasar.

Ya bayyana cewa, “Wannan shi ne dalilin da ya sanya Shugaban Kasa tun a wancan lokaci ya yanke shawarar rufe iyakokin kasar har zuwa yanzu da aka bude su a makon jiya.

“Muna ci gaba da tattauna wa da makwabtanmu domin su bayar da hadin kai wajen ganin an dakatar da kwararowar ’yan ta’adda, makamai, muggan kwayoyi da yin fataucin mata amma lamarin ya ci tura sabanin tsammanin da shugaban kasar ya yi.

“Wannan shi ne dalilin da ya tilasta shugaban kasar na ba da umarnin rufe iyakokin kasar.

“A bisa gwaji yanzu mun sake budewa da fatan cewa yarjejeniyar da muka kulla da su za ta yi tasiri wajen ganin mun yi aiki tare kafada-da-kafada da hukumomin tsaronmu, wanda a dalilin haka ya sanya ba mu bude iyakokin gaba daya ba.”

“Za mu ci gaba da gwada wa mu gani, idan an cimma nasara, za a bude sauran iyakokin, idan kuma akwai matsala to kuwa dole ne Gwamnati ta sake nazari da yin karatun ta nutsu.”

A ranar Laraba, 16 ga wata Dasimban 2020 ne ’yan Najeriya suka yi lale maraba da izinin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar na bude wasu iyakoki hudu na kan tudu a kasar nan.

Daga cikin iyakokin da Gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin budewa tun bayan rufe su a watan Agustan bara sun hadar da ta Seme da ke Jihar Legas, iyakar Illela da ke Jihar Sakkwato, Maigatari da ke Jihar Jigawa, sai kuma iyakar Mfun da ke Jihar Kuros Riba.