✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fadar Shugaban Kasa ta yi barazanar sake dawo da dokar kulle

Sai dai ya ce an kirkiro dokar ne da kyakkyawar manufa ba wai don a musgunawa mutane ba.

Fadar Shugaban Kasa ta yi barazanar sake dawo da dokar kulle a karo na biyu, matukar ‘yan Najeriya suka ci gaba da watsi da matakan kariyar COVID-19, musamman sanya takunkumi.

Babban Mai Taimakawa Shugaban Kasa kan Harkokin Watsa Labarai, Malam Garba Shehu ne ya yi gargadin a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Garba Shehu ya ce, “Yayin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen sake kulle kasa domin tilasta bin matakan kariya kamar yadda Kwamitin Kar-ta-kwana na yaki da cutar.

“’Yan Najeriya su kwana da shirin cewa wannan annobar ba wai kawai barazana ce ga lafiyar kasa da mutanenta ba, har ma da tattalin arziki da ma kowanne sashe na rayuwarmu,” inji shi.

Ya ce ko a makon da ya gabata sai da shugaban ya rattaba hannu a kan wata doka da za ta tilastawa ‘yan Najeriya bin matakan kariyar tare da hukunta wadanda suka yi kunnen uwar shegu da su.

Sai dai ya ce an kirkiro dokar ne da kyakkyawar manufa ba wai don a musgunawa mutane ba.

A cikin dokar dai, duk wanda aka kama yana yawo babu takunkumin rufe fuska zai iya fuskantar hukuncin daurin watanni shida a gidan yari.