✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fadi-tashin farfado da noman auduga a Abuja shekaru 40 bayan daina yin sa

Bara ne Kungiyar Manoma da Masaya Auduga ta Kasa (COPMAN) reshen Abuja ta sake dawo da noman auduga a yankin Birnin Tarayya shekara 40 bayan…

Bara ne Kungiyar Manoma da Masaya Auduga ta Kasa (COPMAN) reshen Abuja ta sake dawo da noman auduga a yankin Birnin Tarayya shekara 40 bayan da aka daina yin sa.

Kungiyar ta yi wannan hobbasa ne a karkashin tsarin Babban Banki Najeriya (CBN) na ba wa manoma rance, sai dai kuma shirin ya zo da kalubale da dama wanda ya sa manoma korafi.

Fa’idar shirin ba wa manoma rance na CBN ita ce sama musu rancen kayan aiki da suka hada da takin zamani da iri da maganin kwari da famfon feshi a kan farashi mai rahusa wanda kuma za su biya wannan bashi ne da kaka ta hanyar ba da audugar da suka noma.

Wannan wani yunkuri ne na Gwamnatin Tarayya don ganin ta farfado da noman auduga a cikin kasa ta yadda manoma za su iya samar da audugar da kamfanonin gurza da masaku suke bukata don inganta ayyukansu.

Wata fa’idar wannan shiri kuma ita ce kokarin sama wa dinbim matasa ayyukan yi tay hanyar ba su lamuni don dogaro da kansu ta yadda za a rage masu zaman kashe wando wanda kuma hakan zai inganta harkar tsaro.

Sai dai kuma manona a yankin na Birnin Tarayya sun koka cewa rashin kyakkyawan tsari da rashin kaiwar damina da kuma rashin tsaro sun yi wa wannan sabon shiri karen-tsaye a bara.

Manoman audugar sun kuma koka bisa yadda CBN ya yi masu alkawarin ’yan mata inda a farkon shirin aka alkawarta ba su rancen kudi don su biya ’yan kwadagon da za su yi musu aiki a gonakinsu amma daga karshe ko biyar ba ta shiga aljihunsu ba.

Usman Surajo Baba daga Gwagwalada yana daya daga cikin wadanda damina ta kayar a bara a fannin noman auduga.

Haka kuma ya dandana kudarsa a hannun masu garkuwa da mutane yayin da suka yi garkuwa da shi a cikin gonarsa a lokacin cin auduga.

Usman ya yaba da wannan yunkuri da gwamnatin take yi na tallafa wa manoma don maido da noman auduga a Abuja; Sai dai kuma ya soki rashin kyakkyawan tsarin da shirin ya zo da shi bara.

“Mafi yawan manoman da suke noma kayan sayarwa a Abuja, mun fi sanin noman doya da citta da kuma noman rogo saboda su muka saba, don ba su da wuya sosai, ga riba ga shi kuma da wahala ka yi asara,” inji shi.

Muftahu Munir, Shugaban COPMAN, Reshen Abuja

Dadin baki aka yi mana

“To amma bara sai suka zo mana da maganar noman auduga, suka yi mana zakin baki cewar za su ba mu lamunin kudi da kayan aiki; Ama daga karshe sai suka ba mu kayan aikin amma ba su ba mu ko sisi ba.

“Wannan ce ta sanya sai da na yi ta buge-bugen neman kudin da zan ba wa ’yan kwadagon da suka taya ni aiki a gonata mai girman kadada daya,” inji Usman.

Ya ci gaba da korafi a kan yadda ba a kawo masu iri da da sauran kayan aiki da wuri ba da kuma yadda tabarbarewar tsaro ke kawo wa harkar noma tarnaki.

“Sai da lokaci ya kure suka kawo mana iri da sauran kayan aiki. wannan kuma shi ne dalilin da ya sa audugarmu ba ta yi yabanya da kyau ba.

“Sannan ga shi tsaro ya tabarbare a kasa. Da farkon kaka lokacin da audugata ta fashe, sai na kwashi ’yan aiki a motata na kai su gona don su cinye mini auduga.

“Kwatsam, sai ga wasu mutane dauke da makamai. A nan suka kama ni suka tafi da ni, ba su sako ni ba sai da aka sayar da kadarorina sannan kuma ’yan uwa da abokan arziki suka hada naira N500,000 aka ba su a matsayin kudin fansa.”

Inshorar Manoma ta Kasa (NAIC) ta biya?

Sai Usman ya ce, “Kungiyar COPMAN tun da fari ta fada mana cewa duk ’ya’yanta ta yi masu inshora da Hukumar Inshorar Noma ta Gwamnatin Tarayya (NAIC).

“Amma har yanzu babu wanda ya zo mana da maganar asarar da muka yi ballantana a biya mu; Abin da kawai suka damu da shi shi ne mu biya su bashinsu.”

Shugaban COPMAN reshen Abuja, Malam Muftahu Muhammad Munir a hirarsa da Aminiya ya ce a karkashin wannan kungiya manona da yawa sun rungumi wannan shiri na noman auduga a fadin kananan hukumomin Birnin Taraya in banda Abaji inda suka yi rajista da wata kungiyar daban.

‘Tamkar gwaji ne’

Malam Munir ya ce, “Ka san kokarin da muka yi bara na maido da noma auduga a Birnin Tarayya bayan an daina yin sa kusan shekaru 40, kamar gwaji ne za mu kira shi domin manoman wannan yanki ba su san shi ba a halin yanzu.

“Wadanda suka san shi kuma suna ganin ba shi da riba. A hakan muka samu muka janyo hankalin manoma da dama suka shiga shirin.

“Duk da yake mun fuskanci kalubale da dama amma dai za mu iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu.

“Wannan shiri, CBN ne ya dauki nauyinsa. Inda yake ba wa manoma da suka yi rajista da kungiyoyi kuma suka cika sharuddan rance.

“Ana ba wa manoman rancen iri da taki da maganin kwari da kuma famfon feshi, Kuma za su biya wannan bashi ne da ita kanta audugar da suka noma.

“Idan aka auna audugarka aka cire ta kudin da ake bin ka sauran kuma ita gwamnatin ce za ta saya daga hannunka.”

Kalubalen noman auduga a 2020

Da yake maganar kalubalen da suka fuskanta, Malam Muftahu cewa ya yi, “Mun fuskanci kalubale da yawa. Alal misali, shi kansa irin da za a shuka da kuma sauran kayan aikin duk sun zo mana ne a makare.

“Wannan ne ya sanya muka yi shuka cikin watan Yuni, wato kusan a ce mun makara da kusan wata biyu.

“Sai dai da yake irin yana da kyau sannan kuma ga taki da maganin kwari, kan ka ce kwabo audugar ta girma.

“Amma kuma tana gabar ’ya’ya sai kwatsam ruwan sama ya dauke ba kamar yadda ya saba kaiwa ba.

“Wani abin al’ajabi kuma da ba mu taba gani ba shi ne na rashin samuwar raba bayan daukewar ruwan. Domin bisa al’ada idan ruwan sama ya dauke a kan samu zubar raba har kusan mako biyu.

“Don haka wadannan na daga cikin dalilan da suka sanya mutane ba su samu audugar ba kamar yadda suka zata.”

Malam Mannir ya ci gaba da cewa, “Amma a halin yanzu babban kalubalen da muke fuskanta shi ne na biyan bashi.

“Akwai wadanda suka karbi kayan suka sayar ba su yi noman ba, yanzu lokacin biya ya zo ba auduga ba kayan aikin.”

Ya ce akwai kuma manoman da suka ci gajiyar shirin amma kuma sun yi mirsisi sun ki biyan bashin, saboda a ganinsu shirin wata ganima ce daga cikin tsarin tallafin COVID-19 da gwamnati take ba wa talakawa.

“Irin wadannan manoma sun cinye audugarsu sun kai sun sayar wa wasu ’yan kasuwa daban kuma idan muka yi musu maganar biyan bashin, sai su yi ta tayar da jijiyoyin wuya — Ba auduga, ba kayan aiki, ba kudi kuma babu magana mai dadi.

“Wannan ce ta tilasta mana kokarin kai su gaba don hukuma ta sanya su su biya tilas.

“Yin hakan ya zama wajibi, domin tun farko sai da suka amince da sharuddanmu kafin mu ba su; Sannan kuma sai sun biya ne wasu na baya za su amfana da shirin su ma.”

Batun bada bashin kudi, ani akasi aka samu’
Game da zargin da wasu manoma suka yi na kin biyan kudin inshora ga wadanda suka yi asara da kuma na rashin cika alkawarin ba su bashin kudi, Munir ya ce, “Tabbas an yi mana alkawarin za a ba mu rancen kudi don biyan kudin hayar gona da kuma gyaran gonar.

“Amma mu kanmu ba mu san me ya faru ba aka ki bayar da kudin kuma gaskiya hakan ya sanyaya gwiwar da dama daga cikin manoman

“Maganar inshora kuma, iya sanina dai duk ’ya’yan kungiyarmu suna da inshora da hukumar NAIC, amma ya zuwa yanzu da nake magana da kai babu wani manomi dan wannan kungiya ta COPMAN da ya zo mana da wani korafi na asarar da yake neman inshora.

“Muna nan a shirye muke duk lokacin da aka samu wanda yake da korafi da kuma hujjoji za mu tsaya masa a biya shi.”

A tattaunawarsa da Aminiya ta waya, Mista Rufa’i, wanda jami’i ne na musamman a Hukuman Inshorar Manoma ta Kasa (NAIC) cewa ya yi “Hukuman ita kadai ke da hurumin yi wa manoma rajistar inshora a karskahin Shirin Tallafin ba da Bashi ga manoma na CBN.

“Amma dai an samu wasu kungiyoyin manoma da suka je suka yi rajistarsu da wadansu kamfanonan inshora masu zaman kansu saboda wasu dalilai na kashin kansu.

“Amma idan kana magana ne a kan Kungiyar Manoma da Masaya Auduga ta Kasa (COPMAN), To idan dai har sun yi rajista da NAIC ne, zan iya cewa har ya zuwa yanzu ba mu samu wani korafi daga wurinsu ba.”

Wani manomi daga Hukumar Mulki ta Bwari, mai suna Nura mai Bulo, ya yi korafi kan yadda ya ce COPMAN ta yi masu burum-burum.

Ya fada wa Aminya cewa, “Sun fada mana cewa za su ba mu kudi da kayan aiki.

“Wannan shi ya sanya na ranci kudi na yi hayar katuwar gona na shuka auduga a maimakon masara da na saba shukawa.

“Amma abin haushi ba a bamu ko sisi ba, ga shi kuma audugar ba ta yi kyau ba.

“Ka ga wannan na nufin yanzu dole mu sake neman wasu kudin mu saya wa iyalinmu abinci.”

Karin shawarwari don inganta shirin

Ya kuma zayyano hanyoyin da yake ganin za a bi don inganta wannan shiri, inda yake cewa, “Idan har suna son mu sake yin noman auduga a nan gaba, to tilas sai mun yi gyara a kurakuren da aka samu a bara. In ba haka ba, ba ni, ba sake noma auduga.”

Da yake korafi a kan maganar kasa ba wa manoma rancen kudin kamar yadda aka alkawarta, Nura cewa ya yi “A kan wane dalili ne CBN ya sanya aka karbi lambar asusun ajiyarmu na banki, in har sun san ba za su ba mu kudin ba?”

Shugaban COPMAN, na Hukumar Mulki ta Gwagwalada, Alhaji Shu’aibu ya shaida wa Aminiya cewa shirin ya samu kalubale a Gwagwalada saboda yanayin rashin tsaro da kuma tsadar biyan kudin kwadago.

“Ba mu da tsaro a wannan yankin. Da yawan manoma a nan sai da suka gyara gonakinsu sai makiyaya suka tura musu bisashe suka cinye musu komai.

“Sannan akwai biyu daga cikin ’ya’yan wannan kungiya ta manoma auduga a nan Gwagwalada da aka yi garkuwa da su a gonakinsu.”

Alhaji Shu’aibu ya ba da shawarwarin yadda za a inganta noman auduga inda ya ce, “In dai ana bukatar wannan shiri ya karbu kuma a yi nasara a bana sai an samar wa mutane da tsaro.

“Sannan tilas CBN and COPMAN su hada karfi da karfe suka sun samar da kayan aiki a kan kari.

“Hukumar NAIC kuma ya kamata ta duba kaorafe-korafen manoman da suka yi asara ta biya su.”

Duk kokarin Aminiya don jin ta bakin mai magana da yawun Babban Bankin Najeriya, Mista Osita Nwanisobi, ya ci tura domin ba ya daga wayarsa kuma sakon da aka tura masa ta kafar sada zumunta ta WhatsApp bai amsa ba.