✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fafaroma ya bukaci a tsagaita wuta a Ukraine

Ina fatan ’yan Falasdinawa da dukkanin mazauna wurare masu tsarki za su dandana zaman lafiya.

Jagoran mabiya darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis ya bayyana kaduwa kan yakin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine, inda ya ke fatan ganin an tsagaita bude wuta don samun zaman lafiya.

Fafaroma Francis ya yi amfani da bikin Ista wajen yin kira ga masu fada aji na duniya da su ji koke-koken al’umma kan batun zaman lafiya.

A sakon da ya gabatar a wannan Lahadin albarkacin bukukuwan Ista, Fafaroma ya yi wannan kira ne a daidai lokacin da yaki tsakanin Ukraine da Rasha ke shiga wata na biyu,

Fafaroma ya ce: “Ba abin da muke gani sai zubar da jini da tashe-tashen hankula, zukatanmu cike suke da tsoro da fargaba a yayin da ‘yan uwanmu maza da mata ke rufe kansu don tsira daga hare-haren bama-bamai.”

Ko baya ga batun yakin Ukraine, rikice-rikice a sauran sassan duniya a kasashe irinsu Libiya da Yemen da Afghanistan da Habasha da Barma da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na daga cikin batutuwan da Fafaroma ya mayar da hankali a kansu.

A farkon watan Yulin wannan shekara ne ake sa ran jagoran dariyar Katolika na duniya zai kai wata ziyara a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

Haka kuma Fafaroma Francis ya yi kiran samar da “yanci” a wuraren ibadah a birnin Kudus, bayan artabu tsakanin sojojin Isra’ila da Falasdinawa cikin sa’o’i 48 da ya yi sanadin jikkatar mutane da dama.

“Ina fatan ’yan Isra’ila da Falasdinawa da dukkanin mazauna wurare masu tsarki za su dandana zaman lafiya, su zauna lafiya kuma su shiga wuraren ibada ba tare da wani shamaki ba cikin mutunta ’yancin kowa,” kamar yadda Fafaroma ya bayyana a bikin Ista.