✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fagacin Zazzau ya sallami lauyansa a shari’ar rikicin sarauta

Fagaci ya sallami lauya mai kare shi a karar da Iyan Zazzau ya shigar kan nada Sarki Zazzau

A ci gaba da shari’ar rikicin Sarautar Zazzau da Iyan Zazzau Alhaji Bashar Aminu yake kalubalantar nada Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli Sarkin Zazzau, daya daga cikin wadanda ake kara ya sallami lauya mai kare shi.

Fagacin Zazzau, wanda daya ne daga cikin Masu Zaben Sarki a Masarautar Zazzau ya sanar da sallamar lauyan nasa, Dokta Onyechi Ikpeazu ne ta sakon WhatsApp a lokacin zaman kotun na ranar Juma’a.

Sakon da Barista Alberta Akaahs ya karanta a lokacin zaman kotun don ci gaba da sauraron shari’ar ya ce: “kamar yadda tsarin mulki ya ba wa wanda ake kara na 7 (Fagachin Zazzau) ya zabin lauyan da zai kare shi, to yana amfani da wannan sakon wurin sallamar lauyan.

“Yana kuma rokon kotun ta sallami Dokta Onyechi Ikpeazu da lauyoyin kamfaninsa daga kare Fagacin Zazzau a wanan shari’ar”.

Tuni dai lkalin kotun, Mai Shari Kabiru Dabo ya amince da bukatar da Fagachin Zazzau ya gabatar ta bakin tsohon lauyan nasa.

Lauyan Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu wanda ya shigar ta karar ya shaida wa kotun cewa suna bukatar karin lokaci don isar ta takardu ga bangaren Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli (Sarkin Zazzau), mutum na 11 a cikin wadanda ake kara.

Lauya mai kare Gwamnan Jihar Kaduna, Sakatare Gwamnatin Jihar, da Babban Lauyan Gwamnatin Jihar, wadanda su ne mutum ukun farko da ake kara, ya amince da hakan.

Sai dai lauyan, Barista Chris A. Umar, ya bukaci a ba shi takardun da ke kunshe da bukatun bangaren masu shigar da karar bayan zaman kotun.

Daga nan lauyoyin bangarorin biyu suka bukaci kotu ta bayar ya karin lokaci domin a samu sauraron bukatar Fagachin Zazzau.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Kabiru Dabo ya amince da hakan sannan ya dage zaman zuwa ranar 13 da 14 ga watan Janairun 2021.

Iyan Zazzau na daga cikin mutum uku da suka fi samun yawan kuri’u daga cikin ’yan takarar Sarkin Zazzau na 19 da Masu Zaben Sarkin suka tantance bayan rasuwar Sarki Shehu Idris.

Alhaji Bashar Aminu ya shigar da kara ne yana bukatar kotun ta ayyana shi a matsayin halastaccen Sarkin Zazzau na 19, kasancewar shi ne ya yi zarra a tantancewar da aka yi wa masu neman kujerar.