✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Falalar da ke tattare da azumin watan Ramadan

Azumin watan Ramadan na kunshe da falala mai tarin yawa

Azumin watan Ramadan rukuni ne daga cikin shika-shikan Musulunci, kuma farilla ne da Allah ya wajabta a kan bayinsa.

Azumi yana da falala mai girma, da lada mai yawa ribi-ribi. Allah Madaukakin Sarki ya raba azumi zuwa gare Shi, saboda girmama shi da daukaka shi.

Azumi na da falala mai tarin yawa, amma ga wasu daga cikin su:

  1. A watan Ramadan ana bude kofofin Aljannah, sannan ana rufe kofofin wuta, kuma ana daure shaidanu, zuciya tana fuskantar aikin alheri.
  2. Yin azumi da tsayuwar sallar ashan saboda Allah da neman lada, yana gafarta abin da ya gabata na zunubai.
  3. A cikin watan Ramadan akwai daren Lailatul-Kadari, duk wanda ya tsaya a cikin wannan dare yana mai imani da Allah da neman lada to za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa.
  4. Umara a cikin Ramadan tana daidai da yin aikin hajji tare da Manzon Allah (SAW).
  5. Watan Ramadan watan Alkur’ani ne, a cikinsa aka saukar da shi, don haka ya dace a yawaita karanta shi a cikin wannan wata.
  6. Watan Ramadan wata ne na kyauta da ciyarwa da sadaka.
  7. Baccin mai azumi ibada ne.
  8. Mai azumi yana tare da farin ciki biyu;

                   a. Yayin da ya ke buda baki da,

                  b. Lokacin da zai hadu da Allah (S.W.A).

      9. Azumi garkuwa ne ga wutar Jahannama.

     10. Watan Ramadan wata ne da Allah ke ’yanta bayinsa daga wuta.