✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fallasa: ’Yan majalisa sun karbi kwangila a NDDC

A baya NDDC ta zargi shugaban kwamitin majalisa mai kula da hukumar da karbar kwangiloli.

Ministan Neja Delta, Godswill Akpabio, ya zargi ’Yan Majalisar Tarayya da karbar kwangila daga hukumar kula da yankin (NDDC).

Akpabio ya bayyana haka ne a lokacin da ya bayyana domin amsa tambayoyi a gaban Kwamitin kula da yankin na Majalisar Wakilai, a ranar Litinin.

“Mun bayar da kwangiloli ga ’yan majalisa. Ba lallai ne ki sani ba”, inji shi a lokacin da yake amsa tambayar daya daga cikin ‘yan kwamitin, Boma Goodhead, game da zargin hakan.

A baya kwamitin riko na NDDC ya zargi shugaban kwamitin, Olubunmi Tunji-Ojo, da karbar kwangiloli daga hukumar amma ya karyata.

A ranar Litinin Olubunmi Tunji-Ojo ya sauka daga mukaminsa, yayin da kwamitin ke ci gaba da sauraron bayanai kan zargin badakalar Naira biliyan 81.5 a NDDC.

Kwamitin rikon NDDC karkashin Farfesa Kemebradikumo Pondei ya bukace shi ya ajiye mukaminsa, a lokacin da shi da Akpabio suka bayyana a gaban Kwamitin wanda ya ba su wa’adin ranar Litinin din domin amsa tambayoyi.