✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na kunyata kaina da iyalaina —Fani-Kayode

Tsohon ministan ya ce ya yi nadama yana kuma rokon dan jarida Eyo Charles ya yafe masa

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani Kayode ya ce ya yi abun kunya ga kansa da iyalansa da cin mutuncin da ya yi wa dan jaridar Daily Trust, Eyo Charles a bainar jama’a.

Ya shaida wa taron ‘yan jarida cewa ya yi matukar nadamar munanan kalamai da barazanar da ya yi wa Charles tare da rokon dan jaridar ya yafe masa cin zarafin da ya yi masa kan tambayar da Charles din ya yi masa a lokacin wanin taron ‘yan jarida.

“Ina amfani da wannan dama in roke shi ya yafe min. Na yi abun kunya ga kaina da iyalaina da abokaina da abokan aiki har ma da iyayen gidana da ke gani na da kima sosai.

“Ina matukar takaicin yadda na yi wa dan jaridar. Na zafafa masa sosai. Tambayar akwai dan zolaya a ciki amma sai na harzuka.

“Na yi da na sani; abun ba dadi. Babu shugaba ko fitaccen mutum da zai mayar da martani yadda na yi. Na kunyata kaina. Ina matukar nadama, sannan ina fata hakan ba zai kara faruwa ba”, inji Fani-Kayode.

Fani-Kayode ya yi ta yi wa dan jaridar Daily Trust, Oke Charles munanan kalamai tare da barazanar taba lafiyar jikin Charles, saboda ya yi masa tambaya.

A taron ‘yan jaridar da aka shirya wa tsohon ministan wanda ke zagayen duba ayyukan gwamnoni a yankin Kudu, Charles ya tambaye shi manufar ziyarar duba ayyukan gwamnoin da kuma mai daukar nauyin tafiye-tafiyen.

Ana ganin tambayar na da muhimmanci kasancewar yanzu Fani-Kayode ba jam’in gwamanti ba ne a kowane matake.

Maimakon amsa tambayar, sai ya kama zage-zage tare da barazanar sabauta dan jaridar sannan daga baya wani dogarinsa ya bi Charles ya kara ranaza shi.

Bullar bidiyon irin cin mutuncin da ya yi wa dan jaridar, wanda bai tanka masa ba, ya ja wa tsohon ministan Allah-wadai daga ko’ina tare da neman ya janye dukkannin kalamai da barazanarsa ga Charles.

– Na janye kalmar dakiki

A jawabinsa ga ‘yan jarida a ranar Juma’a, Fani-Kayode wanda abin da ya aikata ya ja masa caccaka daga fadin duniya ya ba wa dan jaridar na Daily Trust hakuri tare bayyana tsananin nadama.

“Babu shugaba ko fitaccen mutum da zai mayar da martani yadda na yi. Na kunyata kaina. Ina matukar nadama, sannan ina fata hakan ba zai kara faruwa ba”, inji shi.

A ranar Laraba, tsohon ministan a wani abu mai a kama da tubar muzuru ya ce janye kalamar ‘dakiki’ da ya yi wa dan jaridar a Kalaba, amma ya musanta yi wa dan jaridar barazana.

Kazalika ya yi mirsisi da amabton sunan dan jaridar ko ma’aiktarsa, lamarin da ake gani a matsayin kunnen kashi.

Nadamar “abu mara dadin” da Fani-Kayode ya ce ya faru na zuwa ne bayan kakkausar suka da ya sha daga hukumomi da kwararru da masu fafutika a fadin duniya.

“Na janye kalmar ‘dakiki’, da na yi amfani da ita a lokacin abin da ya faru tsakanina da wani dan jarida a Kalaba. Ina da abokai da dama ’yan jarida da na taba saba wa sakamakon gajen hakuri ne. Ina nadamar  abun da na yi”, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook da Twitter a ranar Laraba.

Bidiyon yadda ya yi ta tafka wa dan jarida Eyo Charles rashin mutuncin ya karade kafafen sada zumunta tare da haifar da caccaka ga tsohon ministan da taken #bankrolling.

– Yadda abun ya faru

Ya shafe minti kusan biyu yana rashin kyautawar ga dan jaridar da ya kira “sakararai” tare da barazanar taba lafiyarsa, saboda ya tambaye shi game da daukar nauyin tafiye-tafiyen da yake yi na duba ayyukan wasu gwamnoni.

Dan jaridar ya yi tambayar ne kasancewa Fani-Kayode ba jami’in gwamnati ba ne a kowane mataki, amma yake gudanar da ziyarar aikin domin duba ayyukan gwamnonin.

Amma sai ya ce wa jaridar ‘sakarai, dakiki’, ya ci gaba da yi masa barazana da kalamai mara dadi.

“Wane irin dakikanci ne wannan? “Kar ka kuskura ka sake yi min haka. Bani da hakuri, jikinka zai gaya maka”.

– Sai da aka sa baki sannan ya daina

Ya ci gaba da yi wa Charles ruwan ashariya da munana kalamai da kuma barazana, amma dan jaridar bai ce masa uffan ba, sai ma hakuri da ya ba shi.

Sai da Sakatare Watsa Labaran Gwamna Ben Ayade, Christian Ita da sauran ‘yan jarida suka sa baki kafin fusataccen tsohon ministan ya kyale dan jaridar na Daily Trust da Aminiya.

Fani-Kayode sanye da jar hula a wajen taron ‘yan jaridar

– Jami’in tsaro tsohon ministan ya bi sahun dan jaridar

Abin bai tsaya nan ba, domin bayan komawar Kakakin na Jam’iyyar PDP dakinsa na otal, wani daga cikin jami’an tsaon da ke tsaron lafiyarsa ya sake dawowa ya yi wa Charles barazana.

Mutumin ya bi dan jaridar yana caccakarsa a kan tambayar da ya yi wa ubangidansa, har yake tambayar Charles din ko akwai matakin da zai dauka.

Da dan jaridar ya ga abun na iya kazancewa, sai ya ce da jami’in tsaron, “Na ba wa tsohon ministan hakuri.

“Idan amfani da kalmar ‘bakroll’ (daukar nauyi) da na yi ta yi masa zafi to na janye kalmar. Me kake so in yi kuma?”

– Amnesty ta yi tir da cin mutuncin da FKK ya yi wa Charles

Tuni dai kare hakkin bil Adama ta kasa da kasa ta yi Allah-wadaran dabi’ar ta tsohon ministan a matsayin tauyi hakki.

“Amnesty International ta yi tir da barazanar da Femi Fani-Kayode ya yi wa dan jaridar Daily Trust Charles Eyo a Kalaba., inda  Mista Eyo na yin aikinsa.

“Abin da ya wi wa dan jaridar a taron ‘yan jaridar tauye hakkin kafafen yada labarai ni.

“‘Yan jarida na yin tambayoyi ne a madadin al’umma don haka kar a yi musu barazana saboda sun yi tambayar da jama’a ke neman amsa a kai”, inji sanarwar da ta fitar.

– Idan Fani-Kayode ba zai iya ba ya koma gida —SERAP

Ita ma kungiyar rajin yake da rashwa ta SERAP ta yi tir da “ranararwar da cin mutuninc da Fani-Kayode”, ya yi wa dan jaridar sannan ta bukace shi ya bayyana neman yafiya daga dan jaridar.

“Kada wani ya sake ya kira wani dan jarida ‘sakarai’, saboda kawai dan jaridar na yin aikinsa”, inji SERAP.

– ’Yan sanda su ba wa Charles kariya —Daily Trust 

A martanin Media Trust mamallakin Daily Trust da Aminiya, game da abin da ya yi wa dan jaridar, kamfanin ya ce abin da Fani-Kayode abun kyama ne.

Sanarwar dauke da sa hannun Babban Editan Daily Trust Malam Naziru Mikailu ta fitar ta kuma bukaci Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta kasance cikin shirin game da abun da ka iya biyo bayan barazanar da aka yi wa dan jaridar.

Ko kafin nan cibiyar ‘yan jarida ta kasa da kasa IPC ta yi tir da abin da ya yi wa dan jaridar, tare da suka da kakkausan harshe.

– Dole ya gaggauta ba wa Charles hakuri

Cibiyar akin jarida ta kasa da kasa (IPC) ta bakin Babban Darektanta, Lanre Arogundade ta ce ba abun lamunta ba ne abin da aka yi, “Domin ba laifi ba ne don dan jarida Eyo Charles ya yi tambaya cewa tafiyar ta kashin kai ce ko an dauki nauyinta ne.

“Tsohon ministan na da zabin ya ki amsa tambayar wanda hakan zai kawar da yiwuwar cin zarafin da ya yi ba gaira ba dalili a wurin taron.

Sanarwar da jami’in hulda da jama’a na IPC Olutoyin Ayoade ya fitar ta ce, “Tsohon ministan ya gaggauta ba wa dan jaridar hakuri da kuma tabbacin tsaro game sauran barazanar da ya yi masa”.

“IPC ta yi amannan dokar kasa ta dora wa ‘yan jarida alhakin lura da kuam bibiyar yadda ake gudanar da shugabanci tare da yi wa shugabanni tamboyi, saboda haka kada a yi musu barazana a yayin gudanar da aikinsu”, inji shi.

– Ba za mu lamunta ba.

Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), ta ce cin mutuncin da Fani-Kayode ya yi wa dan jaridar “ya nuna kara cewa Fani-Kayode mai motsuwa ne da tsananin kyara kuma ba ya kaunar ‘yan jarida su bibiyi abun da yake yi kuma yana da tsanakin kyara.

Shugaban NUJ Chris Isuguzo ya ce, “Daidai ne ga ‘yan jarida su yi tambaya a kan dalilan tafiye-tafiyen duba ayyukan da yake yi zuwa jihohi, ko da yake har yanzu ba a fayyace a karkashin wace inuwa yake yin ziyarce-ziyarcen ba.

“Halayyar da ya nuna abun kyama ce da ba za mu lamunta ba, kuma muna kiran sa ya gaggaunta janye wannan munanan kalaman da ya yi wadanda suka masu cike da gidadanci.

“Mun yi mamakin Kayode da a baya-bayan nan ya yi amfani da kafafen zumunta wajen kiran shugabanni su yi bayanin abubuwan da suke yi da dukiyoyin jama’a shi ne zai wartaki dan jaridar da ya bukaci bayani game da tafiye-tafiyen da yake yi a fadin kasa, wanda kawo yanzu har ya ziyarci jihohi shida. Wannan abun takaici ne sosai”, inji NUJ.

Husseini Shuaibu, ya ce dole NUJ da Majalisar Editoci su yi tir da “Dagawa da munanan kalaman” da Fani-Kayode ya yi wa dan jaridar, kawai saboda dan jaridar ya yi aikinsa.

“Idan har ba zai iya amsa tambayoyi masu zafi ba saboda ‘gajen hakurinsa’, to ya koma gida ya zauna!”