✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban koma jam’iyyar APC ba —Fani-Kayode

Tsohon ministan ya musanta maganar Gwamna Yahaya Bello cewa ya fice daga PDP

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode ya musanta labarin da Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya bayar cewa ya koma jam’iyyar APC mai mulki. 

A sakon da ya wallafa a yammacin Laraba jim kadan bayan sanarwar ta Yahaya Bello, Fani-Kayode, ya musanta sauya sheka daga jam’iyyarsa ta PDP.

“Duk da cewa mun yi tattaunawar siyasa da ta shafi jam’iyya, amma ban sauya sheka daga PDP ba”, jin Fani-Kayode.

Ya bayyana hakan ne bayan Yahaya Bello yayin sabunta rajistarsa da jam’iyyar a garin Okene na Jihar, ya ce, “Dan uwanmu kuma abokinmu, Cif Femi Fani-Kayode ya dawo jam’iyyarmu da karsashinsa domin bayar da gudunmuwa don ganin APC ta yi zarra.”

A lokacin, Gwamnan ya ce a matsayin tshoho ministan na tsohon dan APC, zai taka muhimmiyar rawa wajen kawo mata cigaba da nasarori.

“A tuna cewa da Femi Fani-Kayode aka kafa wannan babbar jam’iyya, sabanin fahimta ce ta sa shi komawa wani wuri, yanzu kuma ya yanke shawarar dawowa cikinta.

“Ya tuntube ni kuma bisa nauyin da jam’iyya ta dora min, ba zan taba nuna wa kowa bambanci ba,” inji shi.

A baya-bayan nan, tsohon ministan ya wallafa hotunansa tare da Yahaya Bello a ziyarar da suka kai wa Shugaban Rikon APC kuma Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni a shafinsa na sa da zumunta.

“Na samu alfarmar yin muhimmiyar tattaunawa da Shugaban [Rikon] Jam’iyyar APC, Gwamna Buni na Jihar Yobe da Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi inda muka tattauna kan abubuwan da suka shafi kasa, siyasa da kuma mafitar,” inji sakon da Fani-Kayode ya wallafa ranar Laraba.

Tun lokacin aka yi ta tsokaci kan sakon nasa, inda wasu ke tambaya ko tsohon ministan ya sauya sheka zuwa APC ne.

Sai dai sakon nasa bai bayyana hakan ba, inda ya tsaya a kan cewa tattaunawa suka yi kan hanyoyin ciyar da kasa gaba.