✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fani-Kayode ya shiga uku kan zagin dan jarida

Masu kare hakki da yaki da rashawa sun yi wa tsohon ministan rubdugu kan cin mutuncin

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama a Najeriya Femi Fani-Kayode na ci gaba da shan caccaka bayan ya yi wa wakilin Daily Trust da Aminiya cin mutunci a bainar jama’a.

Bullar bidiyon a ranar Talata na cin zarafin da Femi Fani-Kayode ya yi wa wakilin Daily Trust a birnin Kalabar na Jihar Kuros Riba Charles Eyo ya jawo masa la’anta daga hukumomin da kungiyoyi daga fadin duniya da kuma dubun dubatar jama’a musamman a shafukan zumunta.

A taron ‘yan jarida da yake yi a Kalaba, a ci gaba da ziyarar jihohi da yake yi domin duba ayyukan gwamnoninsu, Charles Eyo ya tambayi tsohon ministan manufar ziyarar da kuma wanda ke daukar nauyin tafiye-tafiyensa.

Amma maimakon bayar da amsa sai kawai Fani-Kayode ya ce wa dan jaridar ‘sakarai, dakiki’.

“Wane irin dakikanci ne wannan? “Kar ka kuskura ka sake yi min haka. Bani da hakuri, jikinka zai gaya maka”.

– Sai da aka sa baki sannan ya daina

Ya ci gaba da yi wa Charles ruwan ashariya da munana kalamai da kuma barazana, amma dan jaridar bai tanka masa ba.

Sai da Sakatare Watsa Labaran Gwamna Ben Ayade, Christian Ita da sauran ‘yan jarida suka sa baki kafin fusataccen tsohon ministan ya kyale dan jaridar na Daily Trust da Aminiya.

Fani-Kayode sanye da jar hula a wajen taron ‘yan jaridar

– Jami’in tsaro tsohon ministan ya bi sahun dan jaridar

Abin bai tsaya nan ba, domin bayan komawar Kakakin na Jam’iyyar PDP dakinsa na otal, wani daga cikin jami’an tsaon da ke tsaron lafiyarsa ya sake dawowa ya yi wa Charles barazana.

Mutumin ya bi dan jaridar yana caccakarsa a kan tambayar da ya yi wa ubangidansa, har yake tambayar Charles din ko akwai matakin da zai dauka.

Da dan jaridar ya ga abun na iya kazancewa, sai ya ce da jami’in tsaron, “Na ba wa tsohon ministan hakuri.

“Idan amfani da kalmar ‘bakroll’ (daukar nauyi) da na yi ta yi masa zafi to na janye kalmar. Me kake so in yi kuma?”

– Amnesty ta yi tir da cin mutuncin da FKK ya yi wa Charles

Tuni dai kare hakkin bil Adama ta kasa da kasa ta yi Allah-wadaran dabi’ar ta tsohon ministan a matsayin tauyi hakki.

“Amnesty International ta yi tir da barazanar da Femi Fani-Kayode ya yi wa dan jaridar Daily Trust Charles Eyo a Kalaba., inda  Mista Eyo na yin aikinsa.

“Abin da ya wi wa dan jaridar a taron ‘yan jaridar tauye hakkin kafafen yada labarai ni.

“‘Yan jarida na yin tambayoyi ne a madadin al’umma don haka kar a yi musu barazana saboda sun yi tambayar da jama’a ke neman amsa a kai”, inji sanarwar da ta fitar.

– Idan Fani-Kayode ba zai iya ba ya koma gida —SERAP

Ita ma kungiyar rajin yake da rashwa ta SERAP ta yi tir da “ranararwar da cin mutuninc da Fani-Kayode”, ya yi wa dan jaridar sannan ta bukace shi ya bayyana neman yafiya daga dan jaridar.

“Kada wani ya sake ya kira wani dan jarida ‘sakarai’, saboda kawai dan jaridar na yin aikinsa”, inji SERAP.

– ‘Yan jarida sun yi wa tsohon minista rubdugu

Cibiyar akin jarida ta kasa da kasa (IPC) ta bakin Babban Darektanta, Lanre Arogundade ta ce ba abun lamunta ba ne abin da aka yi, “Domin ba laifi ba ne don dan jarida Eyo Charles ya yi tambaya cewa tafiyar ta kashin kai ce ko an dauki nauyinta ne.

“Tsohon ministan na da zabin ya ki amsa tambayar wanda hakan zai kawar da yiwuwar cin zarafin da ya yi ba gaira ba dalili a wurin taron.

Sanarwar da jami’in hulda da jama’a na IPC Olutoyin Ayoade ya fitar ta ce, “Tsohon ministan ya gaggauta ba wa dan jaridar hakuri da kuma tabbacin tsaro game sauran barazanar da ya yi masa”.

“IPC ta yi amannan dokar kasa ta dora wa ‘yan jarida alhakin lura da kuam bibiyar yadda ake gudanar da shugabanci tare da yi wa shugabanni tamboyi, saboda haka kada a yi musu barazana a yayin gudanar da aikinsu”, inji shi.

Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), ta ce cin mutuncin da Fani-Kayode ya yi wa dan jaridar “ya nuna kara cewa Fani-Kayode mai motsuwa ne da tsananin kyara kuma ba ya kaunar ‘yan jarida su bibiyi abun da yake yi kuma yana da tsanakin kyara.

Shugaban NUJ Chris Isuguzo ya ce, “Daidai ne ga ‘yan jarida su yi tambaya a kan dalilan tafiye-tafiyen duba ayyukan da yake yi zuwa jihohi, ko da yake har yanzu ba a fayyace a karkashin wace inuwa yake yin ziyarce-ziyarcen ba.

“Halayyar da ya nuna abun kyama ce da ba za mu lamunta ba, kuma muna kiran sa ya gaggaunta janye wannan munanan kalaman da ya yi wadanda suka masu cike da gidadanci.

“Mun yi mamakin Kayode da a baya-bayan nan ya yi amfani da kafafen zumunta wajen kiran shugabanni su yi bayanin abubuwan da suke yi da dukiyoyin jama’a shi ne zai wartaki dan jaridar da ya bukaci bayani game da tafiye-tafiyen da yake yi a fadin kasa, wanda kawo yanzu har ya ziyarci jihohi shida. Wannan abun takaici ne sosai”, inji NUJ.

Husseini Shuaibu, ya ce dole NUJ da Majalisar Editoci su yi tir da “Dagawa da munanan kalaman” da Fani-Kayode ya yi wa dan jaridar, kawai saboda dan jaridar ya yi aikinsa.

“Idan har ba zai iya amsa tambayoyi masu zafi ba saboda ‘gajen hakurinsa’, to ya koma gida ya zauna!”