✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Faransa da kawayenta za su fara janye sojojinsu daga Mali

Fararan da kawayenta na kasashen Tururai sun sanar da janye dakarunsu da suka girke a kasar Mali

Fararan da kawayenta na kasashen Tururai sun sanar da janye dakarunsu da suka girke a kasar Mali a ranar Laraba.

Hakan na zuwa ne a yayin da Shugaban Kasar Faransa, Emmanuel Macron, ke kai ziyarar aiki ta kwana biyu a birnin Brussels na kasar Belgium dangane da aikin dakarun a yankin Sahel.

Sojojin rundunar Barkhane ta Faransa da takwarorinsu na Takuba na kasashen Turai da na kasar Burkina Faso sun shafe kimanin shekara 10 a Mali suna taimaka wa dakarun kasar wajen yakar mayakan Jihadi.

Sanarwar da kasashen kawancen suka fitar ta ce za su fice daga Mali ne saboda  cikas da suke samu daga sojojin da suka yi juyin mulki a kasar, ya sa ba sa samun amincin ci gaba da zama a kasar.

Rundunar ta ce, “Sun yanke shawarar janye sojojinsu da kayan soji da ke yankin kasar Mali.”

Tun lokacin da aka fara girke dakarun rundunar Barkhane na Faransa a yankin Sahel, sun yi ta fama da matsaloli, inda aka kashe 53 daga cikinsu.

A 2013 ne dai Faransa ta fara girke sojojinta a Mali domin yakar masu tayar da kayar baya, amma har yanzu haka ba ta cim-ma ruwa ba.

Sai dai sun ce ko sun janye daga Mali, za su ci gaba da da aiki a sauran kasashen Sahel, ciki har da Jamhuriyar Nijar a yankin Tekun Guinea.