✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Faransa ta sallami Shugaban Hukumar Kwallon Kafarta daga bakin aiki

Faransa ta sallami Shugaban Hukumar Kwallon Kafarta (FFF), Noel Le Graet, daga bakin aikinsa.

Faransa ta sallami Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Kasarta (FFF), Noel Le Graet, daga bakin aikinsa.

Kafafen yada labarai sun rawaito wasu majiyoyi a ranar Laraba na tabbatar da sallamar Shugaban.

Rahotanni sun ce an sallami Noel ne bayan wani taron gaggawa na manyan jami’an hukumar, sannan suka sanar da maye gurbinsa da Mataimakinsa, Philippe Diallo, a matsayin Shugaban rikon kwarya.

Mai kimanin shekara 81, Noel, a ’yan kwanakin nan ya sha fuskantar matsin lamba kan zarge-zargen cin zarafi da kuma lalata da mata da kuma wasu zarge-zarge da tsohon fitaccen dan wasan kasar, Zinedine Zidane ya yi masa, kodayake ya sha musanta su.

Zarge-zargen dai sun ja hankalin ’yan wasa da manyan ’yan siyasar kasar. (Reuters/NAN)