✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Faransawa na zaben sabon Shugaban Kasa

Fafatawar za ta fi zafi ne tsakanin Emmanuel Macron da marine Le Pen

An bude rumfunan zabe a kasar Faransa don zaben sabon Shugaban Kasa a daidai lokacin da Shugaba mai ci, Emmanuel Macron, ke neman wa’adi na biyu.

An dai fara kada kuri’a ne tun misalin karfe 8:00 na safe, kuma za a ci gaba da zaben har zuwa misalin 8:00 na dare, lokacin da ake sa ran fara samun sakamakon zaben.

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Kasar ta ce ya zuwa tsakar rana, kimanin kaso 25.5 cikin 100 na masu kada kuri’a ne kacal suka fito zabe, sabanin kaso 28.5 din da suka fita a zaben shekarar 2017.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai, dukkan ’yan takara a zaben sun kada kuri’a, in ban da Shugaba Macron.

Fafatawar dai za ta fi zafi ne tsakanin Macron din da babbar abokiyar hamayyarsa, Marine Le Pen, wacce da ita ce ya fafata a zaben wa’adinsa na farko.

Yayin da akasarin yakin neman zaben Macron ya fi mayar da hankali a kan manufofin Faransa a kasashen waje, musamman yakin Rasha da Ukraine, ita kuwa Marine ta fi mayar da hankali ne a kan harkokin cikin gidan kasar, musamman tsadar kayayyaki, wacce masu zabe suka ce ita ce babbar matsalarsu.

Gidan talabijin din kasar dai zai fara haska sakamakon zaben da zarar an rufe rumfunan zabe da daddare.

Zaben dai zai maimaita kwatankwacin irin wanda aka fafata tsakanin ’yan takarar a zaben 24 ga watan Afrilun 2017, wanda Macron ya lashe da gagarumin rinjaye.

Akalla masu zabe miliyan 48.7 ne suka yi rajistar zaben a fadin kasar.