✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasuwannin duniya sun tafka asara bayan Rasha ta shiga Ukraine da yaki

Shekara bakwai rabon da farashin danyen mai ya haura Dala 100 a kasuwar duniya.

Kasuwannin hannun jari a kasashen duniya sun samu koma-baya bayan Rasha ta shiga kasar Ukraine da yaki.

A safiyar Alhamis da Rasha ta shiga Ukraine din kuma farashin gangar danyen mai ya tashi zuwa kimanin Dala 105 a kasuwar duniya.

“Sanarwar matakin soji da Rasha ta dauka a Ukraine ya sa farashin gangar danyen mai samfurin Brent tashi zuwa $100,” inji Shugaban cibiyar nazarin hannayen jari ta ING, Warren Patterson.

Rabon da farashin gangar danyen mai ya kai Dala 100 a kasuwar duniya tun shekarar 2014 inda ya kai Dala 101.20 a kasuwannin kasashen Asiya.

Tashin farashin a wannan karon ya haifar da fargabar samuwar karancin mai, kasancewar Rasha ita ce kasa ta biyu wajen yawan samar da danyen mai a duniya.

A cewar Patterson, kasuwar danyen mai za ta ci gaba da zama cikin zullumi tana jiran matakin da kasashen Yamma za su dauka a kan Rasha.

“Wannan rashin tabbas din a kasuwar, wadda da ma can ta yi rauni zai haifar da karuwar farashi,” kamar yadda ya bayyana.

Tasirin Rasha a Turai

Rasha dai ita ce kasa ta biyu a duniya wajen samar da danyen mai, inda take sayar wa matatun mai a kasashen Turai suna tacewa.

Ita ce kuma ta daya wajen samar da iskar gas a kasashen Turai, inda suke samun kashi 35 cikin 100 na iskar gas din suke amfani da shi daga gare ta.

Bugu da kari, tana da iyaka da teku, wanda ya hadada ta kasashe masu yawa a nahiyar Turai.

A kan haka ne masu sharhi ke ganin Rasha za ta iya jure takunkumin tattalin da aka kakaba mata.

A kan haka ne Tarayyar Turai (EU) da kungiyar tsaro ta NATO suka dauki matakan karya tattalin arzikin Rashar bayan ta kaddamar da hare-hare a Gabashin Ukraine.

Girgiza tattalin arzikin Rasha

Fara yakin na ranar Alhamis ke da wuya farashin danyen mai ya yi tashin gwauron zabo, kasuwannin hada-hadar hannayen jari kuma suka yi kasa a kasashen duniya.

Ita kanta Rasha, darajar kudinta, wato Rubble, ya karye a kasuwar canjin kudade, sannan kasuwar hada-hadar hannun jarinta ya yi kasa da kashi 20 cikin 100.

Bugu da kari, ’yan sa’o’i kadan bayan Rasha ta kadamar da harin a safiyar Alhamis, Tarayyar Turai (EU) ta kakaba mata takunkumin karya tattalin arziki.

Shugabar Hukumar EU, Ursula von der Leyen, ta ce, matakan, “Za su shafi muhimman bangarorin tattalin arzikin Rasha, ta hanyar katse su daga ci gaban zamani da manyan kasuwanni mau muhimmanci ga Rasha.

Za mu gurgunta cibiyar tattalin arzikin Rasha tare da hana ta damar tafiya da zamani; Za mu kwace kadarorin Rasha da ke kasashen EU, tare da katse huldar bankunan kasar da kasuwar hada-hadar kudaden Tarayyar Turai.

“Kamar yadda muka dauki matakin a baya, har yanzu muna tare da kasashen Amurka, Birtaniya, Kanada, da kuma Japan da Australiya da sauransu a kan wanna batu.”

Kazalika kungiyar tsaro ta NATO ta umarci Rasha ta gaggauta janye sojojinta daga kasar Ukraine.

Kawo yanzu dai babu wani mataki ko takunkumi da aka sanya kai-tsaye ga bangaren danyen mai da iskar gas na kasar.

Dalilin mamaya a Ukraine

A safiyar Alhamis ne Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya umarci sojoji da su kutsa Gabashin Ukraine, da ke neman ballewa daga Ukraine din, su yi ragargaza babu kakkautawa.

Ministan Harkokin Wajen Rahsa, Dmytro Kuleba, ta shafinsa na Twitter, kasarsa ta kaddamar da hare-haren ne a kan yankunan Ukraine da ta ce suna da karfin kai mata hari.

Hakan ne ya kai ga barkewar yaki tsakanin kasashen biyu, Kawo yanzu dai harin ya yi ajalin kimanin mutum 100 da suka hada da sojoji da fararen hula daga bangarorin.

Rasha dai na adawa da yunkurin fadada kungiyar tsaro ta NATO, wanda zai ba wa Ukraine damar zama mamba. Tana zargin idan Ukraine ta zama mamba, za ta nemi sako kwato yankin Crimea a ya balle daga kasar a shekarun baya.

Bayan sojojin Putin sun kaddamar da yaki a ranar Alhamis, Tarayyar Turai (EU) da kungiyar tsaro ta NATO suka kakaba wa Rasha takunkumai, tare da kiran ta da ta gaggauta janye sojojinta daga Ukraine.