✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farashin fetur zai kai N234 bayan cire tallafi

Kudin da ake kashe wa tallafi a duk wata ya isa a gina asibitoci 5,500 a wata

Farashin litar man fetur na iya tashi zuwa N234, a yayin da Gwamnatin Tarayya ke kwangaba-kwanbaya kan cire tallafin mai a Najeriya.

Gwamnatin ta ce tana kashe kimanin biliyan N120 a duk wata wajen biyan ’yan kasuwa gibin farashin man da suke sayarwa N162 lita, maimakan asalin fanrashinsa da ya kai N234 .

Shugaban Kamfanin Mai na Kasa, Mele Kolo Kyari ne ya bayyana haka, ya kuma ce gwamnati ba za ta iya dorewa da biya ba, don haka a bar ’yan kasuwa su rika sayarwa yadda kasuwa ta kama, babu ruwan gwamnati.

An dade ana ce-ce-ku-ce kan batun tallafin man a Najeriya inda a lokuta daban-daban gwamnatin ta dauki mabambantan matsaya a kai.

’Yan kasa ke zargin akwai cuta a ciki, masana kuma na ganin tsugune ba za ta kare ba, muddin aka ci gaba da rufa-rufa a kan harkar tallafin.

Sun ce dole sai kasar ta farfado da matatun manta su rika samar da kudaden shiga don farfado da wasu bangarorin tattalin arzikin kasar.

 

Abin da Kyari ya ce

Shugaban NNPC ya ce kamfanin ba zai iya ci gaba da biyan cikon kudin mai don a rika sayar da lita a kan N162 ba.

Bayan Minista a Ma’aikatar Albarkatun Mai, Timipre Sylva ya yi bayani kan kokarin ganin an aiwatar da kudurin dokar mai na PIB, Kyari ya ce kamata ya yi a bar yanayin kasuwa ya rika alkalancin farashin fetur.

Kyari, ya ce NNPC ke biyan cikon kudin a kan duk man da aka shigo da shi Najeriya a kokarin gwamnati na rage wa ’yan kasa tasirin tashin farashin.

Sai dai kuma ya ce ana fitar da shi zuwa wasu kasashe bayan shigowarsa Najeriya kuma gwamnati ta biya tallafi a kai.

“NNPC kadai ke shigo da mai. Muna shigo da shi mu sayar a kan N162. Amma a yanayin farashin a yanzu, ya kai N211 zuwa N234 kowace lita.

“Haka na nufin masu shan mai ba duka farashin fetur suke biya ba, suna shan mai ne amma gwamnati ke wahalar biyan cikon kudin.

“Shi ya sa a farkon bara gwamnati ta cire hannunta a harkar mai wanda ya sa farashin ya kai N145, muka ci gaba da hakan har zuwa watan Satumba.

“Daga baya aka samu rikici tsakaninmu da kungiyoyin kwadago har aka a jingine batun tsame hannun gwamnati gaba daya, cewa a yi kyakkyawan tsari ta yadda ba za a cuci mutane ba.

“Abu na biyu shi ne ba za a bari wahalar tsadar farashin ta kare a kan jama’a ba ta, shi ya sa aka bullo da shirin komawa amfani da man gas a ababen hawa ta yadda farashin kowanne zai zama kusan daidai da juna.”

Fetur din Najeriya a wasu kasashe

Kyari ya ce farashin fetur din Najeriya ne mafi araha a Afirka inda a wasu kasashen farashin lita ya kai N500.

“Wasu kasashen sun ma fi amfani da fetur din Najeriya, kuma mu ke samar da shi ga kusan daukacin Nahiyar.

“Ba za mu iya ci gaba a haka ba, mu ma muna da matsalolinmu. Shi ya sa, dole mu jingine wannan tsari; Ban san yaushe hakan za ta faru ba, amma na san ana tattaunawa kuma gwamnati ta damu kan yadda karin farashi a bangaren sufuri ke tasiri ga sauran bangarorin rayuwa,” a cewarsa.

Kungiyar kwadago za ta dauki mataki

Tuni dai kungiyoyin kwadaga suka yi wa gwamnatin kashedi cewa idan ta kuskura ta kara farashin daga N162 to za ta gane kurenta.

Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) Ayuba Wabba, ya ce ’yan Najeriya ba su san inda za sa kansu ba idan aka kara farashin mai.

Ayuba Wabba ya ce ga shi dama matsalar rashin aikin yi ta addabe su, baya ga hauhawar farashin kayan masarufi da kuma yadda annobar coronavirus ta karya tattalin arzikin mutane sun addabe su.

“Mun ga yadda alkaluma ke nuna hauhawar farashin kaya; Idan aka yi karin, farashin abubuwa za su ninku, wanda kuma zai yi mummunan tasiri kan ’yan kasa.

“Babban aikin gwamanti shi ne tabbatar da kare ’yan kasa daga fada cikin yanayin da ba sa so,” inji shi.

Wabba ya ce muddin aka kara farashin fetur, “Tabbas za mu tuntubi mutanenmu kan matakin da za mu dauka na gaba.

“Idan ta kai makura mu shiga yajin aikin, za mu tattauna da su kan abin za mu yi.”

Ya cigaba da cewa “’Yan Najeriya ma ya kamata su fito su mara mana baya kar su amince. Mu shugabannin ’yan kwadago mu man ’yan Najeriya yi.”

Dole gwamnati ta yi wa kanta adalci —Masana

Game da kwangaba-kanbaya da gwamnati ke yi kan tallafin fetur, Manajan Daraknta kamfanin Kairos Capital, Sam Chidoka, ya ce, “Ina ganin babbar matsalar ita rufa-rufar da ake yi.

“Da sun ce sun cire tallafin gaba daya; daga baya suka dawo sake cewa ba gaba daya aka cire ba.

“Idan aka cire gaba daya dole a samu bambancin farashi a fadin kasar nan. Amma gwamnati ke biya don cike wannan bambancin; Gaskiya akwai ayar tambaya.”

Chidoka ya kara da cewa idan aka yi lura da karin farashi lantarki da ka yi, da faduwar darajar Naira da hauhawar farashi da kashi 17%, babu hikimar neman kawo karin farashin fetur.

Shugaban Kungiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Legas (LCCI) Muda Yusuf ya ce, “Karin farashin wani reshe ne janye tallafin wanda ya ki ci ya ki cinye wa.”

Ya ce babu makawa dole sai wata ran gwamnati ta daina biyan tallafi, amma mafita ta wucin gadi ita ce, “A samar da wata kafa da za a rika sayar da shi a farashi mai rangwame.

“Tun da NNPC na da gidajen mai a fadin kasar nan, abin ya zo da sauki, sai a yi amfani da su wurin sayarwa a farashin mai rangwame, ’yan kasuwa kuma a bari su sayar da nasu yadda kasuwa ta kama.

“Amma tattalin arzikin Najeriya ya sha wahala saboda kokarin kayyade farashin.”

 

‘Rashin zurfin tunanin gwamnati ne ya jawo’

Wani masanin tattalin arziki a Abuja, Simon Samson Galadima, abu ne mai kyau yadda NNPC ta fito ta bayyana cewa tana biyan tallafin bayan gwamnati ta ce ita ta daina.

“Gara a yi amfani da biliyoyin da ake kashewa a bangaren samar da tsaro, gina makarantu, inganta bangare kimiyya da kere-kere, wadata asibitoci da kayan aiki da kuma zuba jari a bangaren kirkira da inganta rayuwa,” inji shi.

Ya kara da cewa ya kamata a sayar da matatun man gwamnati ko a bayar da hayansu, ko a sayar da hannun jarinsa.

A nasa bangaren, wani kwararre a bangaren makamashi, Michael John, ya ce sakacin da kasar ta yi a baya ne ya jefa cikin hali da ta tsinci kanta a yanzu.

“Da shugabanni sun yi amfani da ribar da aka samu na mai, da ba ma cikin wannan mawuyacin hali.

“Da muna da lafiyayyun matatun mai, babu abin da zai sa mu rika maganar biyan tallafi.

“Kudin tallafin da ake magana, da su za a yi amfani da su wajen ayyukan na bunkasa rayuwa kamar gina hanyoyi da samar da ruwan sha.

“Gwamnati ta lalubo hanyar tace mai a cikin gida ta yadda za a rika samun kudade a sauran bangarorin kasa domin a halin yanzu ’yan Najeriya ba su da karfin aljihu kuma idan aka cire tallafin mai farashin abubuwa za su yi tashin gwauraon zabo,” inji shi.

Ayyukan da za a iya yi da N120bn

Aminiya ta gano cewa N120bn da ake kashewa duk wata kan tallafin ya fi kasafin shekarar 2021 na Jihar Yobe na N106.9bn. Jihar Osun ma kasafinta na shekarar N109bn ne, Ekiti kuma N109.6bn.

Idan aka yi da N120bn na tallafin a wata, to a kowane wata za a gina cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 5,500 a fadin Najeriya.

Kowanne daga cibiyoyin kuma za a kashe masa Naira miliyan 22 bisa kiyasin da Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta Kasa (NPHDA) ta yi  musu a 2017.

Idan aka yi haka, kowacce daga jihohin Najeriya 36 da Yankin Birnin za ta samu cibiyar kula da lafiya 151.

Gidaje 40,000 a duk wata

A 2019 ne gwamanti ta ce akwai bukatar samun gidaje 22 domin cike gibin da ake da shi na gidaje a Najeriya.

Bisa lissafinta na cewa kowane gida za a gina shi a kan Naira miliyan uku, za a iya gidan gidaje 40,000 da N120bn na tallafin mai a kowane wata.

 

Za a rage karanacin ajujuwa da 15.5%

Idan da za a ware wa Hukuamr Kula da Ilimi a Matakin Farko (UBEC) N120bn din tallafin, za ta yi rukuni 8,500 na ajujuwan hudu-hudu, ajujuwa 35,000 ke nan a wata.

UBEC ta kiyasta kudin gina irin wadannan ajujuya a kan Naira miliyan N13.5.

Daga Sagir Kano Saleh, Muideen Olaniyi, Zakariyya Adaramola, Simon E. Sunday, Idowu Isamotu, Faruk Shuaib (Abuja) da Sunday M. Ogwu (Legas)