✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farashin gangar danyen mai ya haura $71.28 a kasuwar duniya

“Muna harsashen karuwar farashin man na wucin gadi zuwa sama da $70 zuwa tsakiyar 2021.”

A karon farko a cikin shekarar 2021, darajar danyen mai ya karu a kasuwar duniya inda farashin kowacce ganga ya haura $71.28.

Hakan na zuwa ne bayan taron Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur na Duniya (OPEC) da sauran mambobin kasashe a ranar Alhamis wanda ya ki amincewa da matsin lambar kara adadin gangunan da suke hakowa a kowacce rana.

Farashin gangar dai ya karu ne da $1.28 (karin kaso biyu cikin 100) zuwa $63.98 a kan kowacce ganga a ranar Larabar da ta gabata.

Norbert Rücker, wani mai fashin baki a bankin kasar Switzerland na Julius Baer a ranar Laraba ya yi harsashen cewa akwai yuwuwar fasashin ya haura $70 kafin tsakiyar shekara.

“Muna harsashen karuwar farashin man na wucin gadi zuwa sama da $70 zuwa tsakiyar 2021,” inji shi.

Muna tafe da karin bayani…