✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Farashin kilon kifi ya yi tashin gwauron zabi a Kano

"Yanzu haka daga lokacin Corona an kara mana kusan naira 1050 zuwa 1100 kan kowane buhu, abincinma ko da kudinka ba ya samuwa ta dadin…

Kungiyar Masu Kiwon Kifi ta Kasa reshen Jihar Kano (PFFAN) ta sanar da kara farashi zuwa N900 kowane kilo.

Kungiyar ta sanar da hakan ne yayin wani zama da ta yi ranar lahadi a Kano.

Jagorancin kungiyar karkashin shugabanta, Nura Ramadan Kabara ya ce, kungiyar ta fitar da sabon farashin ne saboda karin kudin abincin kifi da masu siyar da abinci suka yi musu akan kowane buhu.

Ya ce, “Yanzu haka daga lokacin COVID-19, an kara mana kusan naira N1,050 zuwa N1,100 kan kowane buhu, abincinma ko da kudinka ba ya samuwa ta dadin rai.”

“Dalilan samun karancin abincin da tsadarsa ba zai rasa nasaba da kalubalen rashin tsaro da ake fama da shi a yankunan Arewa, na garkuwa da mutane da hare-haren ‘yan bindiga da ya hana manoma sukuni, uwa uba rashin samun shigo da sinadaran da ake amfani da su wurin samar da abincin ya yi karancin tun lokacin da aka rufe tashoshin jiragen sama a kasar nan,” inji Nura Ramadan.