✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farashin masara ya fadi kasa warwas a Arewa

Hakan ya faru ne duk da farashin wasu kayayyakin na tashi

A yayin da farashin kayan masarufi ke ci gaba da tashin gwauron zabo a Najeriya, farashin masara ya fadi kasa a wasu kasuwannin hatsi na Arewa.

Binciken da Aminiya ta gudanar a Kasuwar Jingir da ke karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato da Kasuwar Saminaka da ke karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna da Kasuwar Sabuwar kaura da ke karamar Hukumar Doguwa a Jihar Kano, ta gano farashin masarar ya fadi kasa warwas.

Aminiya, ta gano buhun masarar da ake sayarwa a watannin Janairu da Fabarairun bana a kasuwannin kan Naira dubu 22,000 yanzu ya dawo Naira 15,000 zuwa 16,000.

Wasu dillalan masara da Aminiya ta zanta da su, sun ce faduwar farashin masarar wani abu ne daga Allah.

Domin tun kaka ake sayen masarar, ba a bari ba har zuwa wannan lokaci da ake ciki. Sarkin Hatsin Saminaka, Malam Manu Isah ya bayyana wa Aminiya cewa, faduwar farashin masara wani abu ne daga Allah.

“Domin idan muka duba, yanzu kusan komai ya yi tsada a Najeriya, sakamakon karyewar tattalin arzikin duniya, musamman idan muka dubi yakin da ake yi a tsakanin Rasha da Ukraine. Wannan yaki ya sa kusan komai ya yi tsada a duniya. Masara ce kawai farashinta ya yi kasa,” inji shi.

Ya ce, bara an noma masara mai yawa, kuma ana sayen masarar, inda har yanzu mutane suna zuwa daga wurare dabandaban suna sayen ta, amma sai ga farashinta ya fadi kasa.

Sai ya nuna tsoron cewa, faduwar farashin masara da tsadar taki za su kawo cikas ga noman ta nan gaba.

Saboda mafi yawan manoma ba su noma masara a daminar bana ba.

“Muna kira ga manoma, kada su ce za su guje wa noman masara, saboda faduwar farashinta. Domin noma dama haka yake, wata rana a samu wata rana a rasa,” inji shi.