✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farashin wake ya yi tashin gwauron zabo

Buhun farin wake ya kai N25,000 a Jihar Taraba

Karancin abin da manoma suka girbe da karancin ruwan sama da tsananin bukata sun sa farashin wake ya yi tashin gwauron zabo a kasuwanni a Jihar Taraba.

Aminiya ta gano cewa karancin ruwan sama a daminar da ta gabata ya haifar da karancin amfanin da manoma suka girbe musamman wake.

Karancin ruwan sama ya sa amfanin da ke gonakin manoma da yawa sun bushe tun kafin su kosa a jihar.

Wani manomi, Alhaji Chindio Makurna ya shaida wa wakilinmu cewa manoma ba su samu girbi mai yawa ba saboda ruwan sama ya yi saurin daukewa.

A cewarsa, masu girbe buhu 50 na wake a gonakinsu a baya, abin da suka samu bana bai wuci buhu 15 zuwa 20 ba saboda amfanin gona ba su gama kosawa ba lokacin da ruwan sama ya dauke.

Makonni kadan bayan girbi, duk da rashin kyan amfanin gona, an sayar da buhum farin wake mai cin kilogram 100 a kan N15,000.

Farashin ya ci gaba da hauhawa, yayin da masu saye da ‘yan sari ke yin tururuwa domin sayen hatsin da a kasuwanni.

Kananan dillalai sun yi ta zuwa kasuwanin hatsi da ke Mutum Biyu, Iware da Maihula suna sayen kayan a kowane mako.

Hakan ya sa farashin buhun wake ya tashi, inda a yanzu ake sayar da shi a kan N25,000.

Jihar Taraba na daya daga cikin manyan masu samar da farin da kuma jan wake a Najeriya, inda kananan hukumomi 14 da ke cikinta ke noma shi da yawan gaske.