✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farfesa Daduut ta zama ’yar takarar APC a Filato ta Kudu

Farfesa Nora Daduut ta Sashen Koyar da Harshen Faransanci na Jami’ar Jos ce, ta lashe zaben fid da takararar zaben cike gurbin kujerar dan Majalisar…

Farfesa Nora Daduut ta Sashen Koyar da Harshen Faransanci na Jami’ar Jos ce, ta lashe zaben fid da takararar zaben cike gurbin kujerar dan Majalisar Dattawa mai wakilatar mazavar Filato ta kudu,  a Jihar Filato karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Farfesa Nora Daduut ta lashe zaben ne, bayan da ta kayar da wadanda suka fafata da ita a takarar.

Za a gudanar da zaben cike gurbi na Sanata a mazabar ne, sakamakon rasuwar tsohon Sanatan da ke wakiltar ta, Sanata Ignatius LongJan a wata Fabarairun da ya gabata.

Da yake bayyana sakamakon zaben, Shugaban Kwamitin Shirya Zaven, Habu Isa Ajiya ya yi bayanin cewa Farfesa Nora Daduut ta lashe zaben ne da kuri’u 1,936.

Damian Shekarau ya samu kuri’u 61, Farfesa Doknan Shenni ya sami kuri’u 60 sai kuma Farfesa Emmanuel Garba wanda ya sami kuru’u 16.