✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farfesa Isa Hashim: Kano ta sake babban rashi

Kasa da sa’o’i 24 bayan rasuwar Sarkin Rano, Alhaji Tafida Abubakar Ila, an kuma ba da sanarwar rasuwar Jarman Kano, Farfesa Isa Hashim. Farfesa Isa…

Kasa da sa’o’i 24 bayan rasuwar Sarkin Rano, Alhaji Tafida Abubakar Ila, an kuma ba da sanarwar rasuwar Jarman Kano, Farfesa Isa Hashim.

Farfesa Isa Hashim ya rasu bayan ya yi fama da gajeriyyar rashin lafiya yana da shekaru 86 a duniya, kamar yadda wani na kusa da shi kana hadiminsa, Aliyu Harazimi, ya shaida wa Aminiya.

Ya ce da safiyar Lahadi marigayin ya rasu bayan ya yi fama da zazzabi na kwanaki biyu.

“Da aka sanar min rasuwar da safen nan na dauka ma Gwaggo, mahaifiya ta, ce domin ita ke fama da matsananciyar rashin lafiya har da suma, amma ko da na isa gidan sai na tarar Jarma ne ya rasu, yanzu da safen nan muka dawo daga jana’izarsa,” inji shi.

Farfesa Isa Hashim tsohon malamin jami’a ne wanda ya yi shekaru da dama yana aiki da Sashen Nazarin Kimiyyar Siyasa na Jami’ar Bayero ta Kano, kafin ya yi ritaya.

Wasu majiyoyi sun ce jikinsa ya kara tsanani ne bayan da ya samu labarin rasuwar wasu fitattun mutane a Kano, ciki har da abokansa.

A ’yan kwanakin nan dai an samu mace-mace da dama a jihar ta Kano wadanda ba a tantance sanadinsu ba.