✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Farfesa Sule Bello: Shekara 1 da rasuwar masanin tarihi da al’adu

Dalilin ci gaba da dabbaka suna da manufofin Farfesa Sule Bello, da shirin sanya wa Cibiyar Tarihi da Al’adu ta Kano sunansa

Masu iya magana kan ce shekara kwana. A ranar Litinin, 3 ga watan Oktoban 2022 ce masani kuma kwararre a kan harkar tarihi da al’adu a Jihar Kano da ma Najeriya baki daya, Farfesa Sule Bello ya cika shekara daya cif da rasuwa.

Abokan arziki, dalibansa da ma wadanda suka taba yin aiki tare da shi a baya sun bayyana shi a matsayin mutum mai son ci gaba da kuma raya al’adu da tarihi a matsayin hanyar kawo ci gaba.

Wannan ne ma ya sa wadannan rukunin mutanen suka shirya jerin hidimomi don cikar shekara daya da tunawa da ranar da ya koma ga Mahaliccinsa, da nufin ganin an ci gaba da dabbaka manufofin nasa.

Daga cikin abubuwan da aka shirya domin tunawar da shi akwai bajekolin kayayyaki da tarihinsa a Cibiyar Kula da Tarihi da Al’adu ta Jihar Kano, wacce aka fi sani da Gidan Dan Hausa, da kuma laccoci na musamman.

Daga cikin kayyyakin da aka yi bajekolin akwai wasu daga cikin tufafinsa, da takardun karatunsa da kyaututtukan da ya taba samu da kuma abubuwan da yake da sha’awa a kansu na bangaren kade-kaden gargajiya da abinci da kasuwanci da hotuna da ma sauran abubuwa da dama.

Wane ne Farfesa Sule Bello?

Marigayi Farfesa Sule Bello, kafin rasuwarsa shi ne Shugaban Jam’iyyar PRP na kasa, kuma Farfesa a fannin Tarihi a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya a Jihar Kaduna.

Ya yi digirinsa na farko da na biyu da kuma digirin-digirgir a fannin Tarihi a ABUda kuma Jami’ar Rutherford da ke Canterbury a Birtaniya.

Ya taba zama Shugaban Cibiyar Raya Al’adu da Tarihi ta Jihar Kano (HCB) daga 1987 zuwa 1989, sai Shugaban Hukumar Raya Fasaha da Al’adu ta Kasa (NCAC) daga 1989 zuwa 2001.

Ya kuma taba zama Kantoman Hukumar Adana Gidajen Tarihi ta Najeriya (NCMM) a shekarar 1991 da kuma Shugaban Hukumar Al’adu ta Duniya (WCC) daga 1991 zuwa 2001.

Ya rasu ranar 3 ga watan Oktoban 2021 bayan wata gajeruwar jinya, inda ya bar mata biyu da ’ya’ya hudu.

 ‘Muna so mu dabbaka manufofinsa’

A cewar shugaban kungiyar da ta shirya bikin tunawa da marigayin, kuma aboki, makusancinsa, Dokta Yusuf Abdallah, sun shirya bajekolin ne don nuna tarhinsa domin ’yan baya su yi koyi.

“Babban burinmu shi ne mu jawo hankalin duniya baki daya a kan gudunmawar wannan bawan Allah a fagen ilimi da kuma jajircewarsa a fannoni da dama, cikinsu har da harkar muhalli da tarihi da al’adu da taimakon al’umma da kuma bayar da horo.

“Duka wadannan abubuwan muna ganin ya kamata a adana su saboda mutane su yi koyi da su.

“Mun tattara tarihin rayuwarsa zuwa lakcoci da littafi. Akwai wasu fitattun malamai da yanzu haka suke rubutu a kan akidu da tarihinsa. Shi kuma wannan bajekolin zai ci gaba har nan da watan Disamba (wata uku).

“Mairgayi Farfesa Sule mutum ne mai saukin kai da tawali’u. Muna kuma kokarin tattara rubuce-rubucensa domin mu mayar da su littafi guda,” in ji shi.

‘Jagora ne na gari, abin koyi’

Shi ma da yake tsokaci a kan marigayin, Dokta Murtala Muhammad na Jami’ar Kimiyya da Fasaha (KUST) da ke Wudil a Jihar Kano, ya ce Farfesa Sule jagora ne abin koyi, kuma sun wallafa littatafai da dama tare da shi.

Ya bayyana shi a matsayin jajirtacce kuma nagartaccen mutum mai wahalar samu wanda sam ba ya yi wa na kasa da shi kallon hadarin kaji.

“Mutum ne da muke alfaharin samun sa a nan Kano, ya tarbiyyantar da mutane da dama cikinsu har da ni.

“Yana da sha’awar bangarori kamar na al’adu da kasuwanci da tattalin arziki da sauransu da yawa.”

Kaunarsa ga al’adu da gargajiya

Shi kuwa Dokta Munzali Ahmad Dantata, aboki kuma makusancin marigayin, ya ce, Farfesa Sule mutum ne mai son ganin ci gaban al’adun Hausa na gargajiya.

Ya ce, “Ya yi amanna da cewa kowace al’ada, ba wai kawai kida da rawa ba, ya kamata a bunkasa su muddin ana bukatar ci gaba.

“A iya tsawon rayuwarsa, ya yi kokarin wayar da kan mutane da ma gwamnati a kan haka, tun ma kafin ya shugabanci NCAC da NCMM.

“Hatta lokacin da yake a Kano gabanin komawarsa Abuja, ya yaki abubuwa da dama, cikinsu har da rusa badalar Kano saboda tana daya daga cikin abubuwan tarihi kuma ababen tunkahon jihar.

“Saboda haka, muna ganin yanzu ne lokacin da ya dace a dabbaka manufofinsa domin ’yan baya su kwaikwaya,” in ji Dokta Munzali Dantata.

Za mu sanya wa Cibiyar Raya Tarihi da Al’adu ta Kano sunansa —Ganduje

Da yake jawabi a yayin taron gabatar da laccoci a kan marigayin, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce gwamnatinsa za ta sauya sunan Cibiyar Raya Tarihi da Al’adu ta Jihar zuwa sunan Farfesan.

A cewar gwamnan, za a yi hakan ne a matsayin hanya daya ta saka masa kan irin gudunmawarsa  ga cigaban al’adun jihar da ma musamman na cibiyar lokacin da ya shugabance ta.

Ganduje ya kuma ce, “Ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa cibiyar daga wajen kade-kade da raye-raye kawai zuwa cikakken wurin adana tarihi da al’adun mutanen Jihar Kano.

“Za mu kai dokar da ta kafa wannan cibiyar gaban Majalisar Dokokin Jihar Kano don a yi mata kwaskwarima a tabbatar da canza sunan.”

Shi ma da yake jawabi a wajen taron laccocin, Sanatan Kano ta Arewa, Barau Jibrin, ya gode wa masu shirya taron saboda hangen nesansu, inda ya ce hakan zai taimaka wajen zaburar da masu tasowa su yi bakin kokarinsu, saboda sun san za a ci gaba da tunawa da su ko bayan ba ransu.

Sauran mutanen da suka gabatar da makaloli yayin bikin, Farfesa Ali musa da Farfesa Ibrahim Mansur, sun yaba wa marigayin tare da addu’ar Allah Ya jikan sa.