✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farfesa Tanko Ishaya ya zama sabon Shugaban Jami’ar Jos

Zai fara aiki a sabon matsayinsa ranar 1 ga watan Disamba, 2021.

Hukumar gudanarwar Jami’ar Jos, ta amince da zaben Farfesa Tanko Ishaya a matsayin sabon Shugaban Jami’ar.

Hukumar gudanarwar ta amince da zaben sabon shugaban ne a babban taron da ta gudanar a ranar Juma’a.

Kafin wannan sabon mukami da aka zabi Farfesa Tanko Ishaya, shi ne Mataimakin Shugaban Jami’ar ta Jos.

Sabon Shugaban Jami’ar ta Jos, zai kama aiki ne daga ranar 1 ga watan Disamba, 2021.

Shi dai Farfesa Tanko Ishaya a yanzu yana da shekara 57 da haihuwa kuma ya fito ne daga garin Zuru na Jihar Kebbi.