✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Farfesa Umar B. Ahmed ya samu lambar yabo ta kasa

Masanin adabin Hausa da wasan kwaikwayo  Farfesa Umaru Balarabe Ahmed, ya samu lambar yabo ta kasa. Shugaban Hukumar Gudanarwar Majalisar Bada Lambar Yabo ta Kasa,…

Masanin adabin Hausa da wasan kwaikwayo  Farfesa Umaru Balarabe Ahmed, ya samu lambar yabo ta kasa.

Shugaban Hukumar Gudanarwar Majalisar Bada Lambar Yabo ta Kasa, Farfesa Shekarau Yakubu Aku ya ce ana zabo mutanen da ake ba su lambar yabo ne saboda gudunmawar da suka ba da ga ci gaban kasa.

Ya bayyana haka ne a lokacin taron laccar ba da lambar yabo karo na biyu na bana da aka gudanar a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Farfesa Shekarau Yakubu Aku ya ce duk mutanen da aka bai wa lambar yabo ta kasa, mutane ne da suka ba da gudunmawa wajen ci gaban kasa kuma wadanda suka yi fice  a duniya a fannoni daban-daban na rayuwar dan Adam da suka  hada da ilimi da al’adu da kimiyya da fasaha da kere-kere.

Ya ce ana gudanar da taron laccar ba da lambar yabon ne domin bayyana batutuwan da mutanen da aka bai wa lambar yabon suka yi na ci gaban kasa domin janyo hankalin ’yan Najeriya.

Shugaban Hukumar Gudanarwar ya ce daga 1979 zuwa yau, majalisar ta bai wa fitattun ’yan Najeriya 76 lambar yabo ta kasa a cikinsu har da Farfesa Umaru Balarabe Ahmed, wanda ya yi fice a kan bunkasa al’adu da wasan kwaikwayo fasahar wakoki, da adabi da rubuce-rubucen litafai a kan al’adun gargajiyar Hausawa.

Farfesa Aku ya ce, yana daga cikin tsarin majalisar cewa duk mutumin da aka ba shi lambar yabon, ana sa ran ya gabatar da lacca a daya daga cikin manyan makarantun kasar nan, kuma Farfesa Umaru Balarabe Ahmed ya gabatar da tasa laccar ce a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya bayyana irin wasannin da ya kasance a ciki kamar haka ya ce, “Wasan da na fara fitowa a ciki na farko shi ne Wasan Kalankuwa a lokacin da nake makarantar firamare a 1940. Wasan Kalankuwa ya samo asali ne daga sunan Kallon Kowa inda a wasu garuruwa akan yi kwana uku wasu kwana daya don gudanar da bikin.”

Ya ce, “Wasan Kalankuwa an fi yin sa ne a tsakanin al’ummar Hausawa inda akan taru a wani dandali mai girma don gudanar da wasanni da kade-kade da kuma raye-raye na gargajiya tare da gabatar da wakoki irin na al’adu. Wannan Wasan Kalankuwa yana gudana ne a tsakanin matasa wadanda ba su gaza shekarun kasancewa a makaranta ba. Kamar ni na kasance ne mai kai-komo a tsakanin mai sarauta da kuma ’yan mulkin mallaka domin sadar da sakonni.”

“A mataki na biyu na wasannin da na kasance a ciki shi ne bayan shekara 10 a lokacin da nake Kwalejin Barewa da ke Zariya, ba zan iya tuna irin wasannin da na yi ba, sai dai a karshen 1957, na rika tunanin yadda zan nuna sha’awata wajen ganin dalibai sun rika ci gaba da karatu a manyan makarantu amma na samu kaina a wani yanayi da sai da na jira kimanin wata takwas kafin in ci gaba da karatu.

A dan wannan lokaci na samu damar yin aiki a matsayin akawu a Ma’aikatar Ilimi ta Arewa daga watan Fabrairu zuwa Satumba1958 a daidai wannan lokaci ne wani Baturen Ingila mai kula da bangaren watsa shirye-shiryen makarantu ya sanya ni cikin harkar shirye -shiyen rediyo. Baturen mai suna Mista Miks tare da wadansu takwarorina wadanda kuma na ji dadin wannan shiri musamman wasa mai suna ‘Ali going to school’ wato Ali yana tafiya makaranta,” inji shi.

Ya ce “Bayan na kammala aiki da Ma’aikatar Ilimin sai na tsinci  kaina a wasa na uku a 1958 zuwa 1961 lokacin da nake karatu a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a kokarina na samun digiri, daga nan sai na samu wannan dama,sai Allah Ya nufe ni da kasancewa daya da ga cikin wadanda suka shirya wasan Shakespeare’s mai sunaThe Temper.

Saboda yadda na yi shiga da  irin muryar da na yi amfani da ita, sai Madam Sparks, ta nuna cikakken jin dadi tare da yaba mini bisa bajintar da na nuna. Wannan basira da bajintar ta kusa sauya mini tunanin canja karatun  da nake yi a da don zama malami zuwa mai wasan kwaikwayo, sai dai wasikar da Hukumar Bayar da Guraben Karo Karatu ta aika mini da ita a lokacin da na mika bukatar canjin karatu ban samu amincewarta ba don haka sai na hakura. Amma rashin amincewar bai hana ni ci gaba da ra’ayina na gudanar da wasan kwaikwayo ba.”

A karshe ya yi kira ga matasa su kasance masu juriya da hakuri da kuma jajircewa a kan duk wani buri da suka sa a gaba, musamman ga masu rubuce-rubuce a kan adabi da kuma bunkasa al’adun gargajiya da wasannin da suka dace da mu.