✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Farfesa Yahuza ya zama Uban Jami’ar Maitama Sule

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadin Farfesa Muhammad Yahuza Bello a matsayin Uba kuma Shugaban Hukumar Gudanarwa na Jami’ar Yusuf Maitama…

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadin Farfesa Muhammad Yahuza Bello a matsayin Uba kuma Shugaban Hukumar Gudanarwa na Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba  ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin ya kuma ce nadin ya fara aiki ne nan take.

“Farfesa Yahuza ya kammala karatun digirin digir-gir dinsa a bangaren lissafi a Jami’ar Arkansas da ke kasar Amurka a shekarar 1998”, inji sanarwar.

Wa’adin Farfesa Yahuza wanda shi ne Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) tun shekara ta 2015 zai kare ne a karshen watan Agusta, 2020.

Gwamnan ya kuma amince da rada wa titin CBN Kwatas na daura da barikin ‘yan sanda sunan Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Jami’ar Maitama Sule, Malam Sule Yahaya Hamma.

Sule dai ya rike mukamai da dama a matakai daban-daban a jihar Kano, ciki har da Sakataren Gwamnatin Jihar daga shekarar 1979 zuwa 1983.

Ya kuma samu lambar girma ta kasa ta MFR a shekarar 1983.