✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fari ya kassara darajar dabbobi a Kenya

Matsalar fari na ci gaba da tilasta wa makiyayan Maasai a kasar Kenya sayar da dabbobinsu kan farashin da bai taka kara ya karya ba…

Matsalar fari na ci gaba da tilasta wa makiyayan Maasai a kasar Kenya sayar da dabbobinsu kan farashin da bai taka kara ya karya ba don samun abin masarufi.

Hakan na faruwa ne saboda rashin ciyawar da dabbobin za su ci sakamakon rashin ruwan sama wanda hakan ya sanya dabbobin nasu kanjamewa.

Rahotanni daga yankin sun ce, dabbar da a baya ake sayar da ita dubu 60,000 zuwa 65,000 a kudin kasar, yanzu ta koma dubu 1,500.

Galibin makiyayan Maasai sun dogara ne da dabbobinsu wajen samun abin dogaro.

Kenya da makwabtanta Habasha da Somaliya, na fuskantar matsanancin fari wanda irinsa na farko ke nan a cikin shekara 40.

Damina hudu ke nan aka samu a jere ba tare da samun ruwan sama a yankunan ba, lamarin da ya jefa al’ummar yankunan cikin mawuyacin hali.