Farkon damina: Ambaliya ta raba mutum 1,326 da muhallansu | Aminiya

Farkon damina: Ambaliya ta raba mutum 1,326 da muhallansu

    Bashir Isah

Akalla gidaje 463 ne suka lalace baya ga mutum sama da 1,300 da suka rasa muhallansu sakamakon ruwan sama mai karfi da aka samu a farkon daminar 2022.

Wuraren da aka samu wannan iftila’i su ne yankunan kananan hukumomin Obudu da Yala da kuma Ogoja na Jihar Riba, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito.

Jami’in Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) a shiyyar, Godwin Tepikor, ya ce, “A yankin Karamar Hukumar Obudu kadai, mutum 503 ne lamarin ya shafa tare da lalata gine-gine 249 da kuma dukiyar jama’a.

“Haka Karamar Hukumar Yala, mun ziyarci kauyuka biyar da ruwan ya yi wa barna, wato Okpoma da Otuche da Olachor da Idigbo da kuma Igbekurikor.

“Mun kai ziyarar gani da ido ne bayan rahoton neman dauki da Shugaban Karamar Hukumar, Fabian Ogbeche, ya aiko mana.”

Jami’in NEMA ya ce, “Iftila’in da ya auku a yankin a ranar 5 ga Afrilun 2022, ya shafi mutum 486 ne kana ya lalata gidaje 214 hade da dukiyoyi.”

Tepikor ya ce iftila’in da ya auku a yankin Ogoja a ranar ya taba kauyuka da suka hada da Ishibori da Ukelle da Ogboje da kuma Abakpa, inda ya shafi mutum 337 da gidaje da sauran kadarorin jama’a.

Jami’in ya ce a dunkule, iftila’in ya shafi mutum 1,326 sannan ya lalata gidaje 463.

Hakan na zuwa ne duk da cewa yanzu ne daminar bana ta fara kankama, lamarin da ya sa ake zullumin yadda lamarin zai kasance idan aka shiga tsakiyar damina lokacin da aka fi samun ruwan sama.

Maraba: Ambaliya ta hana zirga-zirgar ababen hawa

Sakamakon ruwan sama mai yawa da aka samu a yankin Maraba, Jihar Nasarawa, da ke makwabtaka da Birnin Tarayya, Abuja, an samu ambaliyar a wani sashen babbar hanyar Abuja zuwa Keffi tare da hana ababen hawa zirga-zirga na wani dan lokaci.

Lamarin da ya auku a ranar Litin da misalin karfe 8 na dare, da alama hakan ya auku ne sakamakon rashin ingantattun magudann ruwan gefen hanya da kuma maida magudanan ruwan wurin zuba shara da mazauna yankin suka yi.

Ambaliya ta raba mutane da muhallansu a Imo

A Jihar Imo kuma, mazauna kauyukan Okai da Eziama a Karamar Hukumar Isiala Mbano sun fuskanci iftila’in ambaliya sakamakon mamakon runwan sama ranar Litinin da ta gabata.

Rahotanni daga yankin sun nuna gidaje da dama hade da shaguna da sauransu ne aka yi asarar su sakamakon ambaliyar.

Wani da lamarin ya shafa, Emmanuel Nwike, ya  bayyana cewa, “Ambaliyar ta mamaye gidanmu da shaguna da sauran sassan kauyen Okai da ke Eziama.

“Babu wani dauki da muka samu daga gwamnati, sannan idan lokacin zabe ya zo su bukaci mu zabe su. Barnar ta yi yawa, jama’a sun shiga wani hali.”

Wani bidiyon ambaliyar da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna yadda jama’ar yankin da lamarin ya shafa suke ihun neman a kai musu dauki, yayin da wasunsu ke ta shiga ruwan suna kokarin fito da ‘yan komatsansu da ruwan ya kwashe.

Hashen ruwa mai yawa a Legas

Ko a farkon watan Afrilu, sai da Gwamnatin Jihar Legas ta gargadi al’ummar jihar cewa akwai yiwuwar samun ruwa mai yawa a daminar bana da yawansa ya kai 1,750mm, wanda aka yi hasashen hakan ka iya shafar tattalin arziki da kuma harkokin mazauna jihar.

Kodayake dai Kwamishinan Muhalli na jihar, Tunji Bello, ya ce babu bukatar jama’a su tada hankulansu saboda gwamnatin ta yi tanadin da ya dace don ba da kariya ga rayuka da kuma dukiyoyin jama’a.

Bello ya wadannan bayanan ne a wajen taron manema labarai da gwamnati jihar ta shirya don bayyana musu abin da hasashenta kan daminar bana ya nuna.

Duka wadannan na faruwa ne, duk da cewa yanzu ne daminar bana ta fara kankama, lamarin da ya sa jama’a da dama ke zullumin ko yaya lamari zai kasance yayin da aka shiga tsakiyar damina lokacin da aka fi samun ruwan sama mai yawa.