✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Farman Ali: Matashin da ke kwana a kan bishiya tsawon shekara 8

Farman, ya zama abin mamaki a shafukan sada zumunta bayan wallafa hotunan dakinsa

Wani matashi mai shekara 28 dan kasar Pakistan mai suna Farman Ali ya kafa tarihi inda ya shafe shekara 8 yana kwana a dakin da ya tsara a kan bishiya lamarin da ya jawo ake yi masa lakabi ‘Tarzan of Karachi.’

Farman, ya zama abin mamaki a shafukan sada zumunta a dare daya bayan wallafa hotunan dakinsa da ba a saba gani ba da suka yadu a kafafen sada zumunta, makonni kadan da suka wuce.

Mutane sun yi ta sha’awar saurayin da yake rayuwa a saman bishiya sama da shekara takwas, amma ya ci gaba da bayyana wa duk wanda ya yi tambaya game da rayuwarsa, cewa bai yi hakan don son rai ba.

Bayan ya rasa iyayensa biyu, Farman ya kasance matalauci ta yadda ba zai iya samun ko da daki ba, kuma bayan ya zauna a gefen titi na wani lokaci ne, sai ya yanke shawarar gina tsara daki a wurin da babu wanda zai dame shi ko ya kore shi.

Ya yi daki a saman bishiyar da mutane suka dasa Matashi Farman Ali da ke zaune a babban birnin Pakistan wato Karachi, yana rayuwa ta hanyar sana’ar wanke motoci da yin shara da tsabtace wajen gidajen mutane da kuma yin kayan abinci ga wadansu.

Yawancin abokan cinikinsa suna biyan sa da ruwan sanyi da abinci, kuma ’yan kudin da kyar suke biya masa bukatun yau da kullun, don haka ba ya tunanin samun gidan zama.

Labarin matashin mai shekara 28 ya yadu a Pakistan, inda mutane da yawa ke yaba masa saboda tunaninsa mai zurfi.

Kwanan nan ne Kamfanin Dillancin Labarai na bidiyo na kasa da kasa, Ruptly ya yi hira da shi, inda ya ce ya fara rayuwa ne a wata bishiyar birnin Karachi a matsayin mafita ta karshe.

Ya ce, ya yi duk abin da zai iya yi amma abin ya ci tura. Ya ce ya yi ta rokon ’yan uwa da abokan arziki, amma ba wanda ya taimaki talakan da ba shi da abin yi.

Farman ya ce, ya gina dakinsa a kan bishiyar ce da gora da itace da tsofaffin kofofi da kyallaye don kare kansa daga iska da ruwan sama.

Baya ga katafaren gado, ya kuma samu ya tanadi kwandon wanke fuska a kullum da safe da wata ’yar karamar tanda ta dafa abinci da dumama ruwa, har ma da wata karamar fitila mai batir da cajar wayarsa.

Matashin mazaunin kan bishiyar ya shaida wa manema labarai a Pakistan cewa, ya yi aure a wani lokaci, amma tun da yake ba zai iya samun Rupees 30,000 (Dala 165- daidai da Naira dubu 68 da 557) don zama da matarsa a kowane wata da wannan albashin ba, a karshe ta bar shi.

Farman ya ce ya yi ta kira ga hukumomi su kawo musu agaji, sai dai an yi watsi da shi, ya ce a wannan lokaci ne ya mika wuya, ya nemo mafita ga kansa.

Ya ce fatarsa tana ga Allah Madaukakin Sarki ne kawai.