✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fasa gilashin motar makwabci ya jawo wa matashi daurin wata 8

Kotun ta umarci wanda ake tuhumar da ya biya tara ko ya yi zaman gidan kaso

Wata kotu mai daraja ta daya da ke Abuja, ta yanke wa wani matashi mai shekara 29, Dahiru Muhammad, hukuncin daurin wata takwas a gidan yari bisa samunsa da laifin lalata gilashin motar makwabcinsa.

‘Yan sandan sun tuhumi Muhammad da laifin keta haddi, mugun nufi da kuma aikata barna.

Muhammad ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi kuma ya roki kotun da ta yi masa sassauci.

Alkalin kotun, Sulyman Ola, ya bai wa wanda ake tuhuma zabin biyan tarar N30,000.

Ola, ya kuma umarci wanda aka yanke wa laifin da ya biya wanda ya shigar da karar Naira 195,000 ko kuma a daure shi na tsawon wata uku a gidan yari maimakon biyan tara.

Ola, ya gargadi wanda ake karar da ya daina shiga sabgar da ba ta shafe shi ba.

Tun da farko, lauyan masu shigar da kara, Chinedu Ogada, ya shaida wa kotun cewa, mai shigar da karar, Glory Taiyek, ta kai kara wajen ‘yan sandan Kubwa a ranar 15 ga watan Yuli.

Ogada, ya ce wanda aka yanke wa hukuncin da wanda ya kai karar sun samu rashin fahimta a baya.

Ya ce a ranar 12 ga watan Yuli da misalin karfe 6:30 na yamma, wanda ya aikata laifin ya je gidan mai karar ya doka mata kofar da dutse amma ta ki bude kofar.

Ya shaida wa kotun cewa daga baya wanda aka yanke wa hukuncin ya dawo da karfe 8:30 na dare tare da tsani, inda ya shiga gidan ya karya gilashin mai kofar.

Ogada, ya ce a lokacin da ‘yan sanda ke yin bincike, wanda aka yanke wa hukuncin bai iya bayar da gamsasshiyar amsa kan matakin da ya dauka ba.