✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fasahar 5G ba yin kutse ga layin sadarwar jiragen sama

Babu wani dalili a kimiyyance da ya nuna cewa fasahar sadarwar 5G na iya barazana ga layukan sadarwar jiragen sama

Kamfanonin sadarwa a Najeriya sun ce babu tushe ballantana makama a bayanan masu nuna cewa yin amfani da fasahar sadarwa ta 5G zai kawo kutse ga layin sadarwar sufurin jiragen sama.

Kungiyar Kamfanonin Sadarwa ta Najeriya (ALTON) ta bayyana haka ne ganin yadda ake nuna damuwa cewa amfani da fasahar ta 5G zai kawo kutse gami da barazana ga layin sadarwar jiragen sama.

A bayaninsa, Shugaban kungiyar kamfanonin sadarwar, Injiniya Gbenga Adebayo, ya ce babu wani dalili a kimiyyance da ya tabbatar cewa fasahar sadarwar 5G na iya yin kutse ko kawo wata barazana ga layukan sadarwar jiragen sama.

A sanarwar da ya fitar ranar Laraba da dare, Adebayo ya ce, “Babu 5G ba ta yin barazanar kutse ga layukan sadarwar jiragen sama fiye da irin ta layukan sadarwa da ake amfani da su a yanzu.”

Injiniya Adebayo ya bayyana cewa tazarar tsakanin layukan sadarwar da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta bayar tsakanin layin sadarwar 5G da kuma layin sadarwar sufurin jiragen zama ya kai 400MHZ.

Ya kara da cewa tazarar da NCC ta bayar tsakanin layukan biyu shi ne daidai da abin da dokar Hukumar Kula da Layukan Sadarwa ta Kasa (NFMC) ta tanadar.