✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fasfo: Hukumar Imigireshan za ta soma aiki a ranakun Asabar

Hukumar ta ce ta dauki matakin ne don rage yawan masu bukatar takardun

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ta ba ofisoshinta da ke bayar da fasfo umarnin soma aiki a ranakun Asabar domin rage yawan masu bukatarsa da suka yi yawa a fadin kasa.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Mista Tony Akuneme ya fitar a Abuja a ranar Asabar, a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN).

Shugaban hukumar, Isa Jere, ne ya bayar da umarnin hakan, a cewar sanarwar.

Umarnin ya biyo bayan tarin takardun neman samun fasfon ne a wasu ofisoshin hukumar a wasu jihohi, wanda sanarwar ta ce sun taru ne tun lokacin da aka hana zirga-zirga sakamakon annobar COVID-19.

Jere ya umarci ofisoshin da hakan ta shafa da su soma aikin bayar da fasfon ne daga ranar uku ga watan Disamba, zuwa 28 ga watan Janairun shekarar 2023, kowanne mako daga karfe 10:00 na safe zuwa karfe 2:00 na rana.

“Mun yi hakan ne domin mu biya bukatun jama’a da ke son takardun tafiye-tafiye,” inji Shugaban.

Isa Jere ya kuma ja kunnen jami’ansa da cewa hukumar sa ba za ta raga wa duk wani jami’inta da aka samu da duk wani hali na rashin da’a ba, da kuma nuna rashin sanin ya kamata a yayin aikin.

Laka’ari da umarnin, hukumar ta kuma sauya wa manyan jami’in kula da ofisoshin fasfo na jigawa da na Ibadan wurin aiki, a cewar sanarwar.