✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fashewa mai karfi ta kashe mutum uku a wajen cin abinci a Afghanistan

Wasu mutum 13 kuma sun jikkata a harin

Rahotanni daga Kabul babban birnin Afghanistan sun ce akalla mutum uku sun riga mu gidan gaskiya sakamakon fashewar wani abu a wani wajen cin abinci a ranar Laraba.

Mai magana da yawun ’yan sandan yankin, Khalid Zadran, ya ce wasu mutum 13 sun jikkata a sakamakon fashewar.

Zadran ya kara da cewa, jami’an tsaron Taliban sun dukufa bincike don gano musababbin fashewar.

Da farko dai bayanai sun nuna fashewar ta auku ne a lokacin da ma’aikatan wani kamfanin lantarki da ke kusa suke tsaka da cin abincin rana a inda fashewar ta auku.

Sai dai wata kafar watsa labarai da ke yankin ta ce tukunyar gas ce ta yi sanadiyar fashewar.

Kasar Afghanistan na fuskantar munanan fashe-fashe tun bayan da mulkin kasar ya koma hannun Taliban, wanda galibi masu tsattsauran ra’ayin Islama sukan dauki alhakin hakan.

Ba da dadewa ba wani dan kunar bakin wake ya tashi bam a cikin wani taron jama’a a kofar ofishin jakadancin Rasha da ke Kabul.

Lamarin dai ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutum shida tare da jikkata wasu da dama.