✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fashewar gas: Iyaye sun hana ‘ya’yansu zuwa makarantar da abin ya shafa

Lamura sun fara daidaita a titin Aba da ke Sabon Garin a Jihar Kano bayan fashewar tukunyar gas da ya yi sanadiyar mutuwar mutum tara…

Lamura sun fara daidaita a titin Aba da ke Sabon Garin a Jihar Kano bayan fashewar tukunyar gas da ya yi sanadiyar mutuwar mutum tara da jikkatar wasu da dama tare rushewar gini.

To sai dai da dama daga makarantun yankin sun kasance a rufe saboda iyaye sun hana ’ya’yansu barin gida bisa fargabar jita-jitar cewa wani dan harin kunar bakin wake ne ya tayar da bam ba wai fasewar tukunyar gas ba ne.

wakilin Aminiya day a halarci inda lamarin ya faru ya gano duk da cewa wasu masu sana`o`I da shaguna da ke unguwar sun dawo da hada-hadarsu, makarantu da dama wadanda ke makwaftaka da inda abin ya faru na cigaba da kasancewa a rufe.

Wani mazaunin yankin mai suna Emeka John, ya bayyana cewa “Kamar dai yadda kuke gani makarantun Winners, da Winners Kid Academy, da kuma Fimbal Royal duk ba su dawo bakin aiki ba, amma kuma shaguna duk sun dawo.”

Amma shagunan da suka hada katanga da wurin da lamarin ya faru sun kasance a rufe.

Wani mai shago da ke daura da inda abin ya faru mai suna Ekenna ya ce ranar Laraba ya dawo da bude shago saboda al’amura sun lafa.

Shi ma wani Peter Udoko, mazaunin yankin kuma mai gudanar da sana’a, ya ce ’yarsa na cikin makarantar  Winners Academy lokacin da lamarin ya faru, sai dai Allah Ya kiyaye babu abin da ya same ta.

Makwabtan mai waldan da ya rasu

A hannu guda kuma wasu daga cikin makusantan mai waldar da ya rasu bayan fashewar tukunyar gas din, sun bayyana alhininsu kan rashin sa.

Malam Ibrahim Dawakin Tofa, wanda makwabci ne kuma daya daga cikin aminan margayin, ya ce sun yi magana da shi mintina kadan kafin faruwar lamarin.

“Na wuce shi safiyar ranar na ce mishi zan je na dawo domin mu gana, sai dai Allah Bai yi ba,” in ji shi.

Wani makwabcin na sa mai gyaran janareta ya ce ya yi rashin makwabci na gari.

“Ejike ya zo kamar kullum a ranar da abin ya faru domin fara sana’arsa ta walda, bai sauya kaya ba saboda yana jiran shayin da ya saba saye, sai dai kafin mai shayin ya zo wannan mummunar kaddarar ta auku.

Shugaba Buhari, ta bakin kakakinsa, Garba Shehu, ya mika jaje da ta’aziya ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, tare da kira ga masu ruwa da tsaki da su ba da kulawa ga wadanda suka jikkata.