✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fashewar gas ta yi kisa —LASEMA

Hukumar Agaji ta Jihar Legas (LASEMA) ta tabbatar da mutuwar mutum daya a gobarar da ta tashi a wata tashar iskar gas da asubahin ranar…

Hukumar Agaji ta Jihar Legas (LASEMA) ta tabbatar da mutuwar mutum daya a gobarar da ta tashi a wata tashar iskar gas da asubahin ranar Alhamis. 

Babban Daraktan Gudanarwa an LASEMA, Olufemi Oke Osanyitolu, ya ce gobarar ta kuma lalata gine-gine biyar, a unguwar Baruwa da ke Karamar Hukumar Alimosho.

Ya ce jami’an hukumar na kan aiki ceto da kokarin kashe gobarar ta tashi a wata tashar iskar gas.