✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fashewar mota: Mutum 17 sun mutu, 59 sun jikkata a Ghana

Ana ci gaba da gudanar da aikin ceton mutanen da lamarin ya rutsa da su.

Akalla mutum 17 ne suka rasa rayukansu yayin da 59 suka jikkata a garin Apiyate da ke Yammacin kasar Ghana sakamakon bindiga da wata mota ta yi.

Lamarin ya faru ne a yayin da motar ke dauke da abubuwa masu fashewa ta yi kokarin kauce wa wani babur wanda hakan ya haddasa hatsarin da ya yi ajalin mutane da dama.

Lamarin dai ya afku ne da rana a lokacin mutane suke cikin gudanar da harkokinsu sai kawai suka ji karar fashewar wani abu.

Bindigar da motar ta yi ya jawo asarar dukiyoyin dimbin al’umma a yankin, ciki har da gidaje da shaguna da suka rushe.

Sai dai hukumomin kasar har yanzu ba su tabbatar da adadin wadanda lamarin ya rutsa da su ba.

Masu aikin ceto dai na ci gaba da neman wadanda gini ya danne sannan kuma an ba wa mutanen yankin umarnin barin wurin don ba wa hukumomi damar gudanar da aikin agaji yadda ya kamata.

Shugaban Kasar Ghana, Nana Akufo Addo, ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu tare da yin jaje ga wadanda suka samu rauni.

Sannan ya ce gwamnatinsa za ta tallafa wa wadanda abun ya shafa don rage musu radadin halin da suka tsinci kansu.