✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Fashewar sinadari ya hallaka mutum 1, ya raunata 11 a Kaduna

Ana ci gaba da zaman dar-dar a garin Galadimawa na gundumar Fatika a Karamar Hukumar Giwa ta jihar Kaduna bayan wani sinadari ya fashe

Ana ci gaba da zaman dar-dar a garin Galadimawa na gundumar Fatika a Karamar Hukumar Giwa ta jihar Kaduna bayan wani sinadari ya fashe inda mutum daya ya rasa ransa, 11 kuma suka ji raunuka.

Rahotanni sun nuna cewa fashewar ta auku ne da misalin karfe 4:00 na yammacin Juma’a, ko da yake hukumomi ba su kai ga tantance wanne irin abu ne ya fashe ba.

Wani ganau a inda lamarin ya faru ya shaidawa wakilinmu cewa abin ya fashe ne a dab da wani ofishin ’yan sanda dake yankin.

Ya ce ya tsallake rijiya da baya, domin kiris ya rage shima bai mutu a ciki ba ko ya ji mummunan rauni.

Ya kara da cewa, “Ba mu san mene ne ya fashe ba, Allah dai ya taimake ni na tsallake rijiya da baya, saboda yanzu haka mutum uku na can an garzaya da su asibiti a Zariya bayan sun ji mummunan rauni, yayin da ragowar tara kuma ana ci gaba da duba su a wani asibiti a Galadimawa.”

Kazalika, wani mazaunin yankin ya ce wani aminin sa wanda daya ne daga cikin wadanda aka garzaya da su asibiti a Zariya ya rasu.

Ya ce lamarin ya faru ne dab da wani wuri da mutane ke taruwa domin sayen rake a garin.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar lamarin, ko da yake ta ce mutane 10 ne suka ji raunuka, yayin da bakwai kuma suka ji kananan raunuka kuma tuni aka sallame su daga asibitin, uku kuma aka tura su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya.

Kakakin rundunar, ASP Mohammed Jalige ya ce, “Har yanzu muna kokarin tattara alkaluma domin sanin hakikanin abinda ya haddasa fashewar, da zarar mun sami cikakken bayani za mu sanar da ku.”

Karamar Hukumar Giwa dai da Chikun, Birnin Gwari da Igabi na daga cikin yankunan da suka fi kaurin suna wajen fama da matsalolin tsaro a jihar sakamakon ayyukan ’yan bindiga.