Daily Trust Aminiya - Fashewar Tankar Mai: Doke a sabunta dokar kiyaye hadura —Law
Subscribe

Fashewar Tankar Mai: Doke a sabunta dokar kiyaye hadura —Lawan

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya bukaci a sabunta dokokin kiyaye hatsari, duba da yawan hatsarin tankokin mai da ke aukuwa a kasar nan.

Ya ce sabunta dokokin zai sa a rika bin doka da kuma takaita hatsari a hanyoyi.

“Abin bakin ciki ne irin wannan hatsari ya ci gaba da aukuwa duk da matakai da dokokin kiyaye hatsari da ake da su”, inji sanarwar da kakakinsa, OlaAwoniyi ya fitar.

Ya yi bayanin ne a lokacin da yake jimamin fashewa tankar mai a hanyar Lokoja da ta kashe mutane da dama cikinsu har da kananan yara ’yan makaranta da asarar dukiya mai dimbin yawa.

Shugaba Majalisar ya kuma yi ta’aziya ga iyalan wadanda bala’in ya afka musu da kuma gwamnatin jihar Kogi.

Ya ce samar da matakan da za su rage yawan hatsari wani abu ne da ya kamata masu ruwa da tsaki a harkar sufuri su aiwatar.

“Dole mu kawo karshen yawan hatsarorin da ake samu a hanya”, inji shi.

More Stories